Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Labarai»Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 17, Yuni, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 17, Yuni, 2026

By Ahmad Habib IbrahimYuni 17, 2026No Comments3 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

1. Makinde ya ce a shirye yake ya sadaukar da kansa domin ceto ɗaliban Oyo
Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa a shirye yake ya yi duk abin da ya dace domin tabbatar da sakin ɗalibai da malamai 46 da aka sace a ƙaramar hukumar Oriire. Ya kuma tabbatar da cewa Oyo ba za ta fuskanci irin abin da ya faru da ‘yan matan Chibok ba.

2. Kotun Ɗaukaka Ƙara ta dakatar da soke rijistar ADC
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncin da ya umarci INEC ta soke rijistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu huɗu, har sai an kammala sauraron ƙarar da ke gaban kotu.

3. Kotu ta yanke wa wata mata hukuncin kisa kan laifin ta’addanci
Babbar Kotun Tarayya da ke Katsina ta yanke wa Hauwa’u Mukhtar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun ta da laifin haɗa baki da taimakawa ayyukan ta’addanci.

4. Mahara sun kai hari cibiyar NIPSS, sun kashe jami’an tsaro uku
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari cibiyar NIPSS da ke Kuru a Jihar Plateau, inda suka kashe sojoji biyu da ɗan sanda guda ɗaya da ke bakin aiki.

5. Katsina ta haramta sayar da fetur a jarkoki
Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da sabbin matakan tsaro ciki har da haramta sayarwa ko jigilar fetur a jarkoki domin rage ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

6. Kotu ta soke belin Omoyele Sowore
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta janye belin da aka bai wa Omoyele Sowore bisa zargin bata suna, bayan rashin halartarsa a kotu ba tare da hujja mai gamsarwa ba.

7. Sojoji sun ceto mutane 388 daga hannun masu garkuwa
Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da cewa ta ceto mutane 388, ta kama ‘yan ta’adda 31 tare da kashe 10 a hare-hare daban-daban da aka gudanar cikin makon da ya gabata.

8. Gwamnatin Tarayya ta ware wuraren kiwo 470
Gwamnatin Tarayya ta ce ta gano wuraren kiwo 470 da aka tanada bisa doka domin sake matsugunar makiyaya da rage yawo da shanu a titunan Abuja, Lagos da sauran wurare.

9. Naira ta ƙara ƙarfi a kasuwar bayan fage
Naira ta tashi zuwa N1,389 kan dala ɗaya a kasuwar bayan fage daga N1,400, sai dai ta ɗan faɗi a kasuwar musayar kuɗaɗe ta gwamnati (NFEM).

10. Majalisar Dattawa ta dakatar da hutunta saboda matsalar tsaro
Majalisar Dattawa ta dakatar da hutun da take yi tare da gayyatar sanatoci zuwa wani zama na gaggawa a ranar 23 ga Yuni domin tattauna matsalolin tsaro da sauran muhimman batutuwan ƙasa.

Labaran Safiyar Yau
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 11, Yuni, 2026

Yuni 11, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Juma’a 5, Yuni, 2026

Yuni 5, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 4, Yuni. 2026

Yuni 4, 2026

Comments are closed.

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 17, Yuni, 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 11, Yuni, 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Juma’a 5, Yuni, 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 4, Yuni. 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 3, Yuni. 2026
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.