MAGANAR GASKIYA DANGANE DA FIM ƊIN “ABADAN”
Daga: Ahmad Habib Ibrahim (Films Editor)
Bayan kallon fim ɗin ABADAN, akwai abubuwa masu yawa da suka burge ni, haka kuma akwai wasu wuraren da nake ganin da za a iya ƙara gyara domin aikin ya fi ƙarfi.
Da farko, ina ganin rawar da aka bai wa babban jarumin ba ita ce rawar da ta fi dacewa da shi ba. A ganina, irin wannan role ɗin ya fi dacewa da Adam A. Zango. Duk da haka, jarumin ya yi ƙoƙari sosai wajen fassara halayen da aka ɗora masa.

Game da labarin fim ɗin kuwa, gaskiya ya yi matuƙar birgewa. Sai dai an takaita shi sosai kuma an yi saurin kammala shi. Da ace an mayar da shi mini series mai kusan kashi 5 zuwa 6, da ya fi samun damar bayyana dukkanin muhimman abubuwan da ke cikin labarin.
Wani abin yabawa kuma shi ne yadda kamfanin da ya shirya fim ɗin bai nuna gaggawar neman kuɗi ba wajen sakin aikin. Ba a ga tallace-tallacen magungunan gargajiya ko kayan girki da suka saba katse kallon masu kallo ba. Wannan mataki zai ƙara musu daraja a kasuwar shirya fina-finai, musamman idan suka ci gaba da bin wannan tsari a ayyukansu na gaba.
A bangaren soyayya kuwa, tun bayan fina-finan Kugiya na marigayi Ahmad S. Nuhu da kuma Ruhina na Adam A. Zango, ba a sake ganin fim ɗin soyayya da ya zo da irin wannan tasiri ba.
Haka kuma, fim ɗin ABADAN ya samu karɓuwa sosai a YouTube, har ta kai ga ya yi gogayya da shirin Labarina na Aminu Saira. A wasu lokuta ma, yawan masu kallon Labarina ya ragu sosai idan aka kwatanta da lokacin da ABADAN ya fito.

Sai dai a fannin fasahar daukar hoto, akwai wasu matsaloli da suka rage wa aikin ƙarfi. An samu lokuta da dama na out of focus, tsallen hoto, da kuma matsalar white balance wanda ya sa wasu sassa ba su fito da ingancin da ake bukata ba.
Duk da waɗannan ƙananan kura-kurai, ABADAN ya nuna cewa har yanzu masana’antar Kannywood na da damar samar da ayyuka masu inganci da za su jawo hankalin masu kallo. Haka kuma fim ɗin ya zama wani ƙararrawa ga manyan masu shirya fina-finai da su ƙara himma wajen nazari da inganta ayyukansu domin kada su kasance a baya.
Allah Ya ƙara ɗaukaka masana’antar Kannywood.
