Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Labarai»“Wallahi Taallahi A Gaba Na Husaini Gimba Ya Kashe Dadiyata” – Muhammed Musa

“Wallahi Taallahi A Gaba Na Husaini Gimba Ya Kashe Dadiyata” – Muhammed Musa

By Ahmad Habib IbrahimMay 8, 2026No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

Sabon zargin kisan Dadiyata: Su waye Muhammad Musa da Hassan Gimba?
Sabon ikirarin da Muhammad Musa ya yi cewa ya shaida yadda aka kashe Abubakar Idris Dadiyata ya jawo cece-kuce a Najeriya, musamman ganin tarihin rikicinsa da jami’an tsaro.
Muhammad Musa, wanda aka taba dangantawa da kwamitin sulhu tsakanin gwamnatin Zamfara da ’yan bindiga, ya kasance cikin wadanda jami’an tsaro suka kama tare da gurfanarwa a kotu bisa zargin ta’addanci, garkuwa da mutane, satar shanu da mallakar makamai.
A lokacin kama shi, rundunar ’yan sanda karkashin wani jami’i mai suna Hussaini Hassan Gimba ta fitar da wani bidiyo inda Musa ya bayyana ana zargin yana da alaka da fitaccen shugaban ’yan bindiga, Bello Turji. Sai dai daga baya Musa ya ce an tilasta masa yin wadannan furuci.
Rahotanni sun nuna cewa:

an gurfanar da Musa tare da Bello Turji da wasu mutane a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume da dama,

kuma tun daga lokacin akwai rikici tsakanin Musa da jami’an tsaron da suka kama shi.

Yanzu kuma, a wani sabon zargi mai tayar da hankali, Musa ya yi ikirarin cewa jami’an da suka kama shi ne suka kashe Dadiyata.
Wannan sabon furuci ya sa mutane da dama ke tambayar:

shin sabon bayanin na Musa gaskiya ne?

ko kuma wani bangare ne na rikicin dake tsakaninsa da jami’an tsaro?

Har yanzu babu wata hukuma ko kotu da ta tabbatar da wannan ikirari, saboda haka ana jiran sahihin bincike daga hukumomi domin gano gaskiyar lamarin.
Mutane da yawa na ci gaba da addu’ar Allah ya bayyana gaskiya tare da gano wadanda ke da hannu a batan Dadiyata.

Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

An shiga fargaba bayan barkewar Hantavirus a jirgin ruwa

May 8, 2026

Ana cikin fargaba yayin da kotu za ta fara sauraron karar cancantar Jonathan

May 8, 2026

2027: Zan yi shawara sosai – Jonathan ya nuna sha’awar takarar shugaban kasa

May 7, 2026

Comments are closed.

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • An shiga fargaba bayan barkewar Hantavirus a jirgin ruwa
  • “Wallahi Taallahi A Gaba Na Husaini Gimba Ya Kashe Dadiyata” – Muhammed Musa
  • Ana cikin fargaba yayin da kotu za ta fara sauraron karar cancantar Jonathan
  • 2027: Zan yi shawara sosai – Jonathan ya nuna sha’awar takarar shugaban kasa
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 7, Mayu. 2026
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.