Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 21, Aug. 2025
Labaran Najeriya Na Yau – 21 Ga Agusta, 2025
1. EFCC ta saka tsohon shugaban NNPCL, Mele Kyari, cikin jerin wadanda ake bincike saboda badakalar $7.2bn gyaran matatun mai.
2. Yan Najeriya a kafafen sada zumunta sun soki jami’an da suka halarci TICAD9 a Japan bayan an bar rumfar Najeriya babu mai kula da ita duk da halartar Shugaba Tinubu.
3. Ma’aikatar Harkokin Waje ta tabbatar da rasuwar Jakada Taofik Obasanjo Coker, Konsul Janar na Najeriya a Buea, Kamaru.
4. Gwamnatin Anambra ta kori ‘yan sa kai 8 da suka ci zarafin yar NYSC, Miss Edema Jennifer Elohor.
5. IGP Kayode Egbetokun ya amince da samar da sabbin Area Commands guda 2 da kuma daukaka ofisoshin ’yan sanda 5 zuwa Divisions a Jihar Benue.
6. Fitaccen dan wasan fina-finai, Fabian Adibe (wanda ya fito a Things Fall Apart) ya rasu yana da shekaru 82.
7. Gwamna Seyi Makinde ya amince da ranar 26 ga Satumba a matsayin ranar da za a nada Oba Rasidi Ladoja a matsayin Olubadan na 44.
8. Hatsarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 3 a hanyar Enugu–Abakaliki–Ogoja, bayan motar daukar siminti ta kasa daidaita birki.
9. Rundunar ’Yan Sanda ta Ondo ta cafke mutane fiye da 200 bisa zargin aikata laifuka daban-daban cikin watanni 2 da suka gabata.
10. Shugaban NGF, AbdulRahaman AbdulRazaq, ya ce duk da Najeriya ce babbar kasa a Afirka, zuba jari daga waje bai kai 0.5% na GDP ba, da matsakaicin $2bn a shekara cikin shekaru 10 da suka gabata.