
Trump Ya Ce Ba Zai Tura Sojojin Amurka Ukraine Ba
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ba zai tura sojojin Amurka domin tsare yarjejeniyar zaman lafiya da za a iya cimma a Ukraine ba, duk da cewa a jiya ya nuna yiwuwar hakan.
A hirar wayar tarho da aka yi da shi a Fox News safiyar Talata, an tambaye shi: “Wadanne tabbaci kake da su cewa nan gaba, bayan gwamnatin ka, ba za a samu sojojin Amurka suna kare iyakar Ukraine ba?”
Trump ya amsa da cewa: “To, tabbacin da zan bayar shi ne, ni ne shugaban kasa, kuma haka zan tabbatar.”
Wani jami’in Fadar White House ya tabbatar cewa Trump yana da tsayayyen ra’ayi na kin tura sojojin Amurka zuwa Ukraine, sai dai ya kara da cewa akwai wasu hanyoyin da Amurka za ta iya tallafawa Kyiv don ta samu kariya. Ya ce tattaunawa kan batun tabbacin tsaro na ci gaba tsakanin Amurka, ƙasashen Turai da kuma Ukraine.
Shugabannin ƙasashen duniya suna neman sanin irin matakan da Trump zai ɗauka don tabbatar da cewa idan an kulla yarjejeniyar zaman lafiya, Rasha ba za ta sake ƙarfafa kanta ta mamaye ƙarin yankuna ba.
Trump ya kuma ce ƙasashen Turai sune “layin farko na kariya” daga barazanar Rasha, amma Amurka za ta taka rawa wajen tabbatar da tsaron yankin.
Tun farko, Trump ya yi kamfen ɗin neman zaɓensa ne da alƙawarin gujewa tura sojojin Amurka cikin rikice-rikicen ƙasashen waje, lamarin da wasu daga cikin mambobin gwamnatinsa ma suka goyi baya ta hanyar rage rawar Amurka a yaƙin Ukraine.