
Takaitattun Labaran Safiyar Yau Litinin 18, Aug. 2025
Labaran Najeriya Na Yau – 18 ga Agusta, 2025
1. Akalla ’yan kasuwa 30, ciki har da mata, ake zargin sun rasu a wani hatsarin kwale-kwale da ya auku a ranar Lahadi a kauyen Kojiyo, karamar hukumar Goronyo, jihar Sokoto. Rahotanni sun bayyana cewa mutanen na kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako-mako ta Goronyo ne lokacin da kwale-kwalen da ke ɗauke da fasinjoji da kaya ya kife misalin ƙarfe 1:30 na rana.
2. Sarkin Zuru na jihar Kebbi, Manjo Janar Muhammadu Sani Sami (mai ritaya), wanda aka fi sani da Gomo II, ya rasu yana da shekara 81. Marigayin ya rasu a asibiti a birnin Landan a ranar Asabar bayan gajeriyar rashin lafiya. Ya bar mata huɗu da ’ya’ya bakwai.
3. Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) reshen Kano ta yi watsi da sakamakon zaɓen sake yin kuri’a na majalisar dokoki a mazabar Ghari/Tsanyawa, tana zargin an tafka magudi da kuma haɗin baki tsakanin ’yan siyasa da jami’an hukumar INEC. Shugaban jam’iyyar na jihar, Comrade Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya ce INEC ta hana ’yan ƙasa damar zaɓensu, bayan ta ayyana ɗan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
4. Hukumar NDLEA ta cafke shahararren dillalin miyagun ƙwayoyi, Sunday Ibigide, a Asaba, jihar Delta, bayan farautar da ta ɗauki tsawon shekaru uku. An kama shi tare da mataimakinsa Clement Osuya (27) yayin da suke ƙoƙarin jigilar tulin tabar wiwi guda 250 masu nauyin kilo 138 a cikin motar rarraba kaya. Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya ce Ibigide yana ta gudun hijira tun watan Maris 2022 bayan kama kilo 24.1 na wiwi da gram 10 na “molly” da aka danganta masa.
5. Rundunar ’yan sandan jihar Edo ta sanar da cafke wani ɗan sanda tare da wasu fararen hula uku bisa zargin yin fashi da makami da kuma cuwa-cuwa a birnin Benin. An bayyana waɗanda ake zargin da Inspector Ojo Oloruntobi, Charles Onah, Joseph Ohis, da Enoma Agho. Rahotanni sun ce su ne ke da alhakin jerin fashi da cuwa-cuwa da cin zarafin jama’a a cikin garin.
6. Hukumar INEC ta bayyana zaɓen kujerar majalisar jihar Zamfara a mazabar Kaura-Namoda South a matsayin wanda bai kammala ba, saboda matsaloli a rumfunan zaɓe guda biyar. Jami’in tattara sakamakon, Farfesa Lawal Sa’adu, ya bayyana hakan da misalin ƙarfe 1:30 na safe, inda ya ce matsalolin a unguwannin Sakajiki da Kyambarawa ne suka tilasta wannan mataki.
7. Jam’iyyar APC ta gode wa ’yan Najeriya bisa irin goyon bayan da suka nuna mata wanda ya kai ga samun nasarori a zaɓen cike guraben ’yan majalisa da aka gudanar a jihohi 12 na ƙasar. Kakakin jam’iyyar na ƙasa, Mista Felix Morka, a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Lahadi, ya danganta wannan nasara da amincewar jama’a ga jagorancin Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu.
8. Jam’iyyar APC ta yi watsi da sakamakon zaɓen kujerar majalisar dattawan Anambra ta Kudu da aka gudanar ranar Asabar. INEC ta bayyana Dr Emmanuel Nwachukwu na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 90,408. Shugaban APC na jihar Anambra, Chief Basil Ejidike, ya zargi cewa an tsare ɗan takararsu a gidansa ta hannun jami’an tsaron Anambra Vigilance Group.
9. An ruwaito cewa wasu ’yan Najeriya biyu da aka fi sani da Collins da Osas sun mutu a Tripoli, babban birnin Libiya, cikin yanayi da ake kyautata zaton yana da alaƙa da guba. An tattaro cewa mutanen biyu, waɗanda ke zama a Misrata, sun yi tafiya zuwa Tripoli a ranar 20 ga Yuli tare da wani abokinsu da ba a bayyana sunansa ba kafin faruwar lamarin.
10. Wani mummunan hatsari ya auku a ranar Lahadi lokacin da wani motar haya mai ɗauke da fasinjoji ta fada cikin rafin Namnai a ƙaramar hukumar Gassol ta jihar Taraba. Wannan ya bayyana ne a wani rubutu da wani masani kan tsaro, Zagazola Makama, ya wallafa a shafinsa na X. Ya bayyana cewa motar, mai ɗauke da tambarin Adamawa Express, ta yi ƙoƙarin ketare wata gada da ta ruguje kafin afkuwar hatsarin.

