Bincike Ya Bankado Safarar Jarirai a Najeriya

Bincike Ya Bankado Safarar Jarirai a Najeriya

“Gidajen Haihuwa na Tilas” a Najeriya: An Fallasa Safarar ‘Yan Mata da Sayar da Jarirai

Wani bincike mai tsanani ya bankado “gidajen haihuwa na tilas” a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, inda ake sace ‘yan mata kanana, wasu ‘yan shekaru 13, sannan a tilasta musu ciki ta hanyar fyade.

A wadannan gidaje, matan da aka sace ana garkuwa da su har zuwa lokacin da suka haihu, sannan ana sayar da jariranga masu nema da kudi. A wasu lokuta, ana siyar da jaririn ba tare da izini ko sanin mahaifiyar ba, sannan a tilasta mata komawa ciki karo na biyu ko na uku.

Wannan mummunan aikin yana faruwa ne cikin sirri, inda ‘yan kungiyoyin safarar mutane ke samun kudi sosai ta hanyar amfani da karancin tsaro da talauci. An bayyana cewa wasu jarirai na kaiwa kasashen waje, ciki har da Turai, inda ake sayar da su da sunan karΙ“ar Ι—a.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam da hukumomin tsaro sun fara daukar matakai, amma suna fuskantar kalubale wajen gano irin wadannan cibiyoyi da kuma ceton wadanda abin ya shafa.