
YARA 652 SUN RASA RAYUKANSU SAKAMAKON YUNWA A KATSINA – CEWAR MSF
Ciwon yunwa na zama barazana mai girma ga dubban yara a Najeriya, musamman a yankunan da rashin tsaro da talauci suka yi kamari.
Ƙungiyar Doctors Without Borders (MSF) ta bayyana cewa ƙalla yara 652 sun mutu sakamakon ciwon yunwa mai tsanani (malnutrition) a jihar Katsina cikin watanni shida na farkon shekarar 2025. Wannan ya faru ne, a cewarsu, saboda yanke tallafin kudi daga ƙasashen duniya.
“A yanzu muna fuskantar yanke tallafi sosai daga ƙasashe irin su Amurka, Birtaniya, da Tarayyar Turai, kuma hakan yana haifar da matsala wajen kula da yara masu fama da yunwa,” — in ji MSF.
Katsina, da ke arewacin Najeriya, na fama da matsananciyar rashin tsaro da ya tilasta mutane barin gonakinsu, lamarin da ya kara tsananta halin yunwa da ƙuncin rayuwa.
Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UN WFP) ta sanar a ranar Laraba cewa daga ƙarshen Yuli 2025, za ta dakatar da bayar da abinci da kayan kiwon lafiya ga mutane miliyan 1.3 a yankin arewa maso gabas sakamakon ƙarewar kayan ajiya.
Gwamnatin Najeriya ta ware ₦200 biliyan (dala miliyan 130) don rage illar da yanke tallafin kasashen waje ke haifarwa a fannin kiwon lafiya.
MSF ta kara da cewa adadin yara masu matsananciyar yunwa a Katsina ya karu da kashi 208% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Sun ce:
“Abin bakin ciki ne cewa yara 652 sun mutu a cibiyoyinmu tun farkon shekarar 2025.”
‘Yan bindiga da suka addabi Katsina suna ci gaba da hana mutane yin noma da rayuwa cikin kwanciyar hankali. Duk da hadin guiwar gwamnati da ‘yan sa-kai, matsalar ta’addanci da fashi da makami ta ci gaba da addabar al’ummar jihar.