
Takaitattun Labaran Safiyar Yau Talata 5, Aug. 2025
Tinubu Ya Ba D’Tigress Kyautar $100,000 Kowacce
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba ‘yan wasan kwallon kwando mata na Najeriya (D’Tigress) kyautar dala dubu ɗari ($100,000) kowacce saboda nasarar da suka samu. Ya bayyana hakan ne a wajen taron girmamawa da aka shirya musu a fadar shugaban ƙasa, Abuja, ranar Litinin.
Femi Falana Ya Soki Yunkurin Kamfen na 2027
Lauyan kare haƙƙin ɗan adam, Femi Falana, ya soki fara kamfen ɗin zaben 2027 da wuri. A hirarsa da Channels TV, ya bukaci INEC ta tunasar da ‘yan siyasa dokar zabe ta 2022.
WAEC Ta Fitar da Sakamakon Jarrabawar WASSCE Na 2025
Hukumar WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar WASSCE na 2025 ga ɗaliban makarantu. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin.
Sojojin Ritaya Sun Rufe Ma’aikatar Kuɗi da Zanga-Zanga
Wasu tsofaffin sojoji da suka yi ritaya da kansu sun gudanar da zanga-zanga a gaban hedkwatar ma’aikatar kuɗi. Sun fara zanga-zangar ne da misalin 10:15am ranar Litinin.
‘Yan Bindiga Sun Sace Mata 26 a Zamfara
Aƙalla mata 26 aka sace a Zurmi, Jihar Zamfara, a wani sabon hari da ‘yan bindiga suka kai. Wannan ya faru ne kwana ɗaya bayan wani hari da aka kai garuruwa 16 a Kaura Namoda inda aka kashe mutane 5.
Matar Da Ke Da Nakasa Da Wasu 6 Za Su Yi Zaman Gidan Yari Na Shekaru 93
Wata mata da ke da nakasa, Rita Idehen, da wasu shida sun samu hukuncin zaman gidan yari na shekaru 93 gabaɗaya, bisa laifukan da suka shafi safarar miyagun ƙwayoyi a jihar Edo.
‘Yan Sanda Sun Kama Masu Hannu a Kisan Lauya a Rivers
Rundunar ‘yan sandan Jihar Rivers ta kama mutane bakwai da ake zargi da hannu a kisan lauya Bright Owhor, wanda aka kashe ranar 5 ga Yuli, 2025.
Gwamna Oyebanji Ya Ayyana Niyar Takarar Zango Na Biyu
Gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya bayyana shirinsa na sake neman takara a 2026, bayan samun goyon baya daga jama’a da jam’iyyar APC.
Tsohon Dan Majalisa Ya Fice Daga APC, Zai Bayyana Sabon Mataki
Shiddi Usman, tsohon ɗan majalisa daga Taraba, ya bayyana cewa zai sanar da sabuwar hanyar siyasar da zai bi bayan ficewarsa daga jam’iyyar APC.
‘Yan Fashi Sun Kashe Jami’in NSCDC a Kasuwar Jigawa
Jami’in NSCDC a Jihar Jigawa ya rasa ransa sakamakon harin wasu ɓarayi a kasuwar mako ta Shuwarin da ke ƙaramar hukumar Kiyawa.