
Takaitattun Labaran Safiyar Yau Litinin 4, Aug. 2025
1. El-Rufai Ya Gargadi Tinubu da APC:
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi gargadin cewa za a lalata hadin kan al’umma gaba ɗaya idan Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC suka sake komawa mulki a 2027. Ya bayyana haka ne a Sokoto yayin gangamin jam’iyyar adawa ADC.
2. D’Tigress Sun Yi Tarihi:
Kungiyar kwallon kwando ta mata ta Najeriya, D’Tigress, sun zama ƙungiyar farko da ta ci kofin FIBA AfroBasket sau biyar a jere bayan doke Mali. Sun samu gurbin kai tsaye zuwa gasar cin kofin duniya ta 2026 a Berlin, Jamus.
3. Peter Obi Ya Ƙara Jaddada Wa’adin Shekara 4:
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a 2023, Peter Obi, ya sake bayyana aniyarsa ta yin wa’adi guda na shekaru hudu idan aka zaɓe shi a 2027. Wannan martani ne ga suka daga Gwamnan Anambra, Chukwuma Soludo.
4. Gini Ya Rufta Kan Mai Hotel:
Wani gini na hotel da ake ginawa a Uromi, Jihar Edo, ya rufta ya kashe mai shi, Andrew Isesere. Ma’aikata sama da 20 sun sha da kyar, wasu kuma sun ji rauni.
5. LASU Ta Dakatar da Jarabawa:
A Jami’ar Jihar Legas (LASU), majalisar jami’ar ta dakatar da dukkan harkokin karatu da al’amuran jami’a, ciki har da jarabawar zangon biyu na shekarar 2024/2025, saboda yajin aikin malaman jami’ar.
6. SDP Ta Maka INEC a Kotu:
Jam’iyyar SDP ta shigar da ƙara kan hukumar zaɓe (INEC) saboda ƙin amincewa da ’yan takararta a zaɓukan cike-gurbi a jihohi 12.
7. ’Dan Limamin Abuja Ya Rasa Ransa:
Attahiru Abubakar, ɗan Chief Imam na Kuchibuyi a Abuja, ya mutu bayan harbin ’yan sanda a rikicin fili, yayin da yayansa Abass ya samu rauni mai tsanani.
8. An Kama Mutanen Benin 10:
Rundunar ’yan sandan Ondo ta cafke ’yan asalin Jamhuriyar Benin 10 da ake zargi da hannu a safarar mutane a jihar.
9. Hasashen Ruwa da Ƙarfin Iska:
Hukumar NiMet ta sanar da yiwuwar ruwan sama mai ƙarfi da guguwa daga Litinin zuwa Laraba, tare da yiwuwar ambaliyar gaggawa a wasu yankuna.
10. PDP Ta Fitar da Jadawalin Zaben Shugabanni:
Jam’iyyar PDP ta sanar da jadawalin babban taron zaben shugabanninta, wanda za a yi a ranar 15-16 ga Nuwamba. Siyar da fom za ta fara 3 ga Satumba zuwa 22 ga Satumba, sannan mayar da fom zai kasance kafin 26 ga Satumba.