
Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 22, Oct. 2025
Labaran Najeriya Na Yau – 22 Ga Oct, 2025
1. An ƙona sakatariyar jam’iyyar ADC a Ado-Ekiti
Wasu da ake zargin ’yan daba ne suka ƙona sakatariyar jam’iyyar ADC da ke yankin Basiri, Ado-Ekiti a daren Litinin. Wuta ta lalata kujeru, kayan ofis, lasifika da sauran kayan aiki.
2. Kotu ta soke zaɓen kananan hukumomi a Ebonyi
Babbar kotun tarayya da ke Abakaliki ta soke zaɓen kananan hukumomi da aka gudanar a watan Yuli 2024 a Jihar Ebonyi. Mai shari’a Hillary Oshomah ya ce zaɓen bai bi tanadin dokar zaɓe ba.
3. Gobarar mota mai ɗauke da fetur ta kashe mutane a Neja
Mutane da dama sun mutu a mummunar fashewar tankar mai da ta faru a hanyar Agaie–Bida, kusa da Essa, a ƙaramar hukumar Katcha, Jihar Neja. Gobarar ta haddasa cunkoson ababen hawa sosai.
4. Tinubu ya nada sabon Minista daga Jihar Plateau
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Dr Bernard Mohammed Doro daga Jihar Plateau a matsayin Minista. Nadinsan na jiran amincewar majalisar dattawa kafin ya fara aiki.
5. Gwamna Bala Mohammed ya kafa sabbin masarautu 13 a Bauchi
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya rattaba hannu kan dokar da ta ƙirƙiri sabbin masarautu 13 da sarakuna 111 a faɗin jihar. Haka kuma ya soke dokar Sayawa Chiefdom tare da kafa Zaar Chiefdom da hedkwata a Mhrim Namchi.
6. Lauyan Nnamdi Kanu da ’yan uwansa sun shiga gidan yari
Wata kotun majistare a Kuje ta bayar da umarnin tsare lauya Aloy Ejimakor, ɗan’uwan Nnamdi Kanu, da wasu mutum 10 da aka kama a zanga-zangar #FreeNnamdiKanu.
7. Kotun Koli ta dakatar da yanke hukunci kan karar PDP da Tinubu
Kotun koli ta ɗage yanke hukunci a kan karar da jihohin da jam’iyyar PDP ke mulki suka shigar don kalubalantar ayin dokar ta baci da Shugaba Tinubu ya ayyana a Jihar Rivers.
8. Gwamnati ta umarci MDAs su mika asusun su na bankuna
Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya umarci dukkan Ma’aikatu, Hukumomi da Sassa (MDAs) su mika bayanan asusun su da ke bankunan kasuwanci, domin inganta tsarin kula da kuɗi.
9. Dan majalisa Ojema Ojotu ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
Dan majalisar wakilai mai wakiltar Apa/Agatu, Ojema Ojotu, ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu, ne ya karanta wasikar sauya shekar a zaman majalisar.
10. INEC ta ce masu kada kuri’a miliyan 2.8 za su shiga zaɓen Anambra
Hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC, ta ce kimanin miliyan 2.8 na masu kada kuri’a ne za su shiga zaɓen gwamnan Anambra da za a gudanar a 8 ga Nuwamba, 2025.