Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 7, Aug. 2025

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 7, Aug. 2025

Labaran Najeriya Na Yau – 7 ga Agusta, 2025

PDP Zai Yanke Shawara Kan Wike:
Shugaban riko na PDP reshen Kudu maso Kudu, Emmanuel Ogidi, ya ce jam’iyyar za ta yanke hukunci kan halayen Ministan Abuja, Nyesom Wike, mako mai zuwa saboda halayyarsa da ba su gamsu da ita ba.

Soja Ya Kashe Dan Sanda a Taraba:
Soja sabo mai suna Dauda Dedan ya sare dan sanda mai suna Aaron John a Jalingo har lahira. Lamarin ya faru a unguwar Mayo-Goyi da misalin karfe 9 na dare a ranar Litinin.

Femi Falana: Siyasa Ta Zama Hannun Barayi:
Lauyan kare haƙƙin dan Adam, Femi Falana (SAN), ya bayyana cewa siyasar Najeriya na hannun ‘yan daba da barayi, yana mai korafi kan talauci da lalacewar ababen more rayuwa a kudu maso yamma.

Naira Ta Ƙara Ƙarfi a Kasuwar Bayan Fage:
Naira ta ƙara ƙarfi zuwa N1,550/$ a kasuwar bayan fage, daga N1,565/$. Sai dai a kasuwar canjin kuɗi ta NFEM, ta fadi zuwa N1,537.2/$.

Uwargidan MKO Abiola Ta Rasu:
Dr. Doyin Abiola, tsohuwar daraktar jaridar National Concord kuma matar marigayi MKO Abiola, ta rasu. Ita ce mace ta farko da ta zama editan jarida a Najeriya.

WAEC Ta Sha Caccaka Kan Matsalar Binciken Sakamako:
Hukumar WAEC ta fuskanci suka bayan da aka rufe shafin duba sakamako saboda “matsalolin fasaha”, lamarin da ya fusata dalibai da iyaye, musamman saboda rashin nasara a jarrabawar Ingilishi.

Ana Bincike Kan Mutuwar Wani a Coci a Akwa Ibom:
Wani mutum mai suna Udeme Uko ya mutu bayan an harbe shi a cikin coci a karamar hukumar Ukanafun, da misalin karfe 12 na dare. Yana kwance da iyalinsa lokacin da ‘yan bindiga suka kai farmaki.

Peter Obi Ya Kira Da Gina Jam’iyyu Masu Ƙarfi:
Tsohon dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi, ya ce lokaci ya yi da za a gina jam’iyyu masu inganci fiye da gwamnati. Ya bayyana haka yayin gabatar da littattafai guda biyu kan siyasar Najeriya.

Hatsarin Jirgin Soja a Ghana Ya Hallaka Ministoci:Jirgin sama na soji ya yi hatsari a yankin Ashanti na Ghana, inda mutane 8 suka mutu ciki har da Ministocin Tsaro, Edward Boamah da Muhalli, Ibrahim Mohammed.Gwamnati Na Bukatar N3 Trillion Don Gama Tituna:
Ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na bukatar N3tn don kammala ayyukan tituna da NNPCL ke daukar nauyinsu kafin ta dakatar da tallafi daga 1 ga Agusta.