Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 1, Aug. 2025

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 1, Aug. 2025

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Aiyedatiwa:
Kotun daukaka kara da ke Akure, Jihar Ondo, ta tabbatar da nasarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa a zaben gwamna da aka gudanar ranar 16 ga Nuwamba, 2024. Alkalai uku karkashin jagorancin Justice Yargata Nimpar sun yanke hukunci bisa ga amincewa da nasarar Aiyedatiwa gaba ɗaya.

Karin Girma a Hukumar FRSC:
Gwamnatin Tarayya ta amince da kiran girma ga kwamandojin 51 da mataimaka 49 a hukumar FRSCOlusegun Ogungbemide, mai magana da yawun FRSC, ne ya bayyana hakan.

Ayyukan Wutar Lantarki Na N213.7 Biliyan:
Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da ayyukan wutar lantarki guda biyu da kudinsu ya kai ₦213.7 biliyan domin inganta hasken lantarki a makarantun gaba da sakandire, asibitoci da kauyukaMinistan Wuta, Adebayo Adelabune ya bayyana hakan.

Dino Melaye Ya Fice Daga PDP:
Tsohon Sanata daga Kogi, Dino Melaye, ya fice daga jam’iyyar PDP, yana zargin jam’iyyar da rashin iya jagoranci da samar da ingantaccen mulki.

Mutuwar Malama A Tricycle A Aba:
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar wata mata mai suna Mrs Emmanuel Love Onuora, da ake kira “Aunty Love,” da ta rasu a cikin adaidaita sahu (keke Napep) a Aba, Jihar Abia.

Hatsura a Lekki-Epe:
Hukumar LASTMA ta tabbatar da mutuwar mutane biyar a cikin hatsura biyu dabam-dabam da suka faru a kan titin Lekki-Epe a Jihar Legas, inda wasu biyar suka jikkata.

Ƙarin Masu Sauya Sheƙa Zuwa APC:
Fiye da mambobi dubu goma (10,000) daga PDP a Idanre/Ifedore sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC. Dan majalisar wakilai daga yankin, Festus Akingbaso, ya rigaya ya koma APC.

Nicolas Felix Ya Ce Tinubu Zai Yi Nasara a 2027:
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a APC, Nicolas Felix, ya ce ƙawancen jam’iyyu a ƙarƙashin ADC ba zai iya hana Tinubu lashe zaben 2027 ba, yana mai cewa zai samu akalla milliyan 15 na ƙuri’u.

Jerry Gana Ya Ce Peter Obi Zai Fi Kowane Ɗan Arewa A 2027:
Tsohon Ministan Bayani, Prof. Jerry Gana, ya bayyana cewa idan Peter Obi ya koma PDP, zai doke kowanne ɗan takara daga Arewa a zaben shugaban ƙasa na 2027.

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda da Dama:
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe ’yan ta’adda da dama, kama mutane 15, tare da kwato makamai da kayan soji a fadin ƙasar.