Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 09, Oct. 2025

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 09, Oct. 2025

Labaran Najeriya Na Yau – 09 Ga Oct, 2025

  1. Bankin Duniya ya ce Najeriya ta tabbatar da sauyin tattalin arziki ya amfani talakawaBankin Duniya (World Bank) ya bukaci Najeriya da ta tabbatar da cewa sakamakon gyare-gyaren tattalin arziki da ake yi ya zama abin amfani ga jama’a. Shugaban Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ya bayyana cewa sama da mutane miliyan 139 na rayuwa cikin talauci a kasar, don haka gwamnati ta mayar da hankali wajen sauƙaƙa rayuwar jama’a.

  1. Sojoji sun ceto mutum 37 da aka yi garkuwa da suRundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa dakarunta sun ceto mutum 37 da aka yi garkuwa da su a yayin wani babban farmaki kan ‘yan ta’adda. An kashe ‘yan ta’adda 9, an kama mutane 8, tare da kwace makamai da dama a cikin wannan samame.

  1. Naira ta kara karfi a kasuwaNaira ta karu zuwa ₦1,490/$1 a kasuwar bayan fage, daga ₦1,495/$1 a jiya. Haka kuma a kasuwar musayar kudade ta gwamnati (NFEM), Naira ta karu zuwa ₦1,469/$1, bisa rahoton tattalin arziki na yau Laraba.

  1. Akpabio da Abba Moro sun yi takaddama a Majalisar DattawaShugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da Jagoran ‘Yan adawa, Sanata Abba Moro, sun yi gardama kan yawaitar sauya sheka daga jam’iyyun adawa zuwa APC. Akpabio ya ce rashin tsari a jam’iyyun adawa ne ke sa hakan, sai dai Moro ya mayar da martani cewa adawa za ta ci gaba da tsayawa da kafafunta komai rashi.

  1. Orji Kalu ya ce Tinubu zai sake lashe zabe a 2027Tsohon Gwamnan Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sake lashe zaben 2027, yana mai cewa babu wanda zai iya kayar da shi – ko Atiku AbubakarGoodluck Jonathan, ko Peter Obi.

  1. ’Yan sanda sun dakatar da dokar lasisin gilashin mota mai duhuRundunar ’yan sanda ta dakatar da aiwatar da dokar lasisin gilashin mota mai duhu (tinted glass permit) bayan an ba ta sammaci daga kotu. Mai magana da yawun rundunar FCT, Josephine Adeh, ce ta tabbatar da hakan a wani shirin talabijin.

  1. INTERPOL ta tabbatar da kama dan Najeriya da ya yi damfara ta soyayyaHukumar INTERPOL ta tabbatar da cewa jami’an tsaro a Argentina sun kama wani dan Najeriya mai suna Ikechukwu N., wanda ake zargi da shirya damfara ta yanar gizo ta hanyar soyayya wadda ta shafi mata dubban a kasashe daban-daban.

  1. Wike ya gargadi shugaban AMAC kan sa suna kan tituna ba bisa ka’ida baMinistan FCT, Nyesom Wike, ya gargadi shugaban karamar hukumar AMACChristopher Maikalangu, da ya daina sanya sunaye a tituna da hanyoyi da ba tare da izini daga ma’aikatar babban birnin tarayya ba.

  1. Kotu ta jinkirta sauraron karar EFCC har zuwa Oktoba 9Wata kotu ta musamman a Ikeja ta dage shari’ar EFCC har zuwa ranar 9 ga Oktoba, domin ta yanke hukunci kan sahihancin hujjojin dijital da hukumar ta gabatar. Alkalin kotun, Justice Rahman Oshodi, ya ce ya bukaci karin lokaci don nazarin shaidun da aka gabatar.

  1. Kotu ta kara mako guda ga kwamitin likitoci don duba lafiyar Nnamdi KanuKotun Tarayya a Abuja ta bai wa kwamitin likitocin da ke duba lafiyar jagoran IPOBNnamdi Kanu, karin mako guda, bayan sun kasa kammala binciken lafiyarsa cikin kwanaki takwas da kotu ta diba a baya.