Sojoji Sun Kashe Ƴan Boko Haram 17 a Arewa-Maso-Gabas

Sojoji Sun Kashe Ƴan Boko Haram 17 a Arewa-Maso-Gabas

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da nasarar kashe ‘yan ta’adda 17 na Boko Haram a wata gagarumar fafatawa da ta gudana a yankunan jihohin Borno da Adamawa. Wannan matakin yana daga cikin kokarin gwamnati na kawo karshen ta’addanci a yankin Arewa-Maso-Gabas da ya daɗe yana fama da rikici.

A cewar kakakin rundunar, an kaddamar da wannan farmaki ne bayan samun bayanan sirri da suka tabbatar da kasancewar wasu ‘yan Boko Haram a wasu maboya. An kuma kwato makamai, harsasai, da abinci da ‘yan ta’addan ke amfani da su.

An gudanar da wannan samame ne tare da hadin gwiwar jami’an Operation Hadin Kai, inda aka kai hari a maboyar da ke kusa da garuruwan Madagali da Damboa.

Rundunar sojin ta bayyana cewa wannan nasara wata alama ce da ke nuna cewa rikicin na karasa da kuma cewa rundunar za ta ci gaba da aikin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

“Za mu ci gaba da murkushe ‘yan ta’adda a ko’ina suke. Rundunar sojoji ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya,” in ji kakakin rundunar.