
Shell da Sunlink sun amince da aikin iskar gas na dala biliyan 2 a Najeriya
Kamfanin mai na duniya, Shell, tare da Sunlink Energies, sun amince da sabon aikin haɓaka iskar gas a wajen teku na Najeriya, wanda zai samar da iskar gas ga Nigeria LNG.
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa jarin aikin ya kai kimanin dala biliyan 2, wanda ke nuna tsare-tsaren Shell na faɗaɗa kasuwancin iskar gas (LNG) a duniya da kuma ƙarfafa matsayinta a Najeriya, duk da ƙalubale da ta fuskanta a cikin shekaru da suka gabata.
A baya-bayan nan, Shell ta sayar da hannunta a filayen mai na cikin ƙasa (onshore) saboda matsalolin zubewar mai da satar man fetur, amma wannan sabon jarin ya tabbatar da cewa kamfanin na da niyyar ci gaba da zuba jari a Najeriya.
A halin yanzu, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) yana da kashi 49% na mallakar Nigeria LNG, yayin da Shell ke da kashi 25.6%, ita ce mai riƙe da kaso na biyu mafi girma.
Sauran masu hannun jari a kamfanin LNG sun haɗa da TotalEnergies da Eni (Agip).
An gano filin HI a shekarar 1985, wanda ke kusan kilomita 50 daga bakin teku da zurfin mitoci 100 a cikin teku.
An shirya fara samar da iskar gas daga wannan fili kafin ƙarshen wannan shekaru goma (kafin 2030).
A cewar Olu Verheijen, mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin makamashi, samar da iskar gas daga wannan fili zai cika kusan kashi ɗaya bisa uku (⅓) na gas ɗin da ake buƙata don aikin Train 7 na Nigeria LNG.
A karkashin yarjejeniyar, Shell Nigeria Exploration and Production Company (SNEPCo) za ta mallaki kashi 40% na aikin, yayin da Sunlink Energies za ta riƙe kashi 60%.
Wannan mataki na Shell ya yi daidai da manufar kamfanin na ƙara yawan samar da iskar gas a duniya da kashi 4 zuwa 5 cikin ɗari a kowace shekara har zuwa 2030.
A watan da ya gabata, Hukumar Gudanar da Albarkatun Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ta amince da cinikayyar dala miliyan 510 da kamfanin TotalEnergies ya yi, inda ya sayar da kashi 12.5% na hannunsa a Oil Mining Lease (OML) 118, wanda ke ɗauke da filin mai na Bonga, ga Shell da Eni (Agip).
Wannan ci gaban yana nuna sabon babi a tsarin kasuwancin iskar gas a Najeriya, tare da fatan ƙara samar da kudaden shiga, ayyukan yi da kuma tallafawa ci gaban tattalin arzikin ƙasa.