
Rahama Sadau Ta Kaddamar Da Bikin Baje-Kolin Fina-finai
Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta ƙaddamar da bikin baje-kolin fina-finan Arewacin Najeriya.
An gudanar da taron fara shirye-shiryen bikin wanda ya samu halarcin ministar raya al’adun Najeriya, Hannatu Musawa da shugaban hukumar fina-finai kuma jarumi a Kannywood, Ali Nuhu da dai sauransu.
Babban abin da bikin ke son cimmawa shi ne nemo hanyoyin fito da ƙwarewar al’ummar arewacin Najeriya.