
Nnamdi Kanu: Sowore da wasu sun gudu yayin da jami’an tsaro suka yi harbi da Borkonon Tsohuwa
Ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan Adam, Omoyele Sowore, wanda shi ne jagoran zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow, ya tsere daga wurin zanga-zangar bayan jami’an tsaro sun bude wuta da borkonon tsohuwa.
Jami’an tsaro — da suka haɗa da ‘yan sanda da sojoji — sun mamaye wurin zanga-zangar tun da misalin ƙarfe 7:00 na safe a ranar Litinin.
A wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, an ga Sowore da wasu masu zanga-zanga suna gudu domin tsira da rayukansu.
Masu zanga-zangar sun shirya ne domin tafiya zuwa fadar Aso Rock domin neman a saki Nnamdi Kanu, wanda shi ne jagoran ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da aka haramta.
Sai dai Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta riga ta gargadi masu shirya zanga-zangar da kada su kuskura su gudanar da wani taro kusa da fadar shugaban ƙasa.