Makomar Peter Obi a jam’iyyun ADC da LP na cikin rudani : 2027

Makomar Peter Obi a jam’iyyun ADC da LP na cikin rudani : 2027

Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, na fuskantar rashin tabbas kan dandalin siyasa da zai tsaya a zaben shugaban kasa na 2027, yayin da ake samun rudani a cikin jam’iyyun da yake da alaka da su.

Rahoton DAILY POST ya nuna cewa Obi, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023 karkashin jam’iyyar Labour Party (LP), na daga cikin manyan jiga-jigan ‘yan adawa da ke shirin haduwa domin hambarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben gaba.

A ranar 2 ga Yuli, 2025, shugabannin adawa da suka hada da Obi, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark, tsofaffin gwamnonin Kaduna da Ribas, Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi, sun amince da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a matsayin dandalin da za su tsaya takara a 2027.

Sai dai, burin Obi na samun tikitin ADC yana raguwa sosai, domin manyan jam’iyyar sun fi karkata zuwa ga Atiku.

Wani tushe daga cikin jam’iyyar ya shaida wa DAILY POST cewa ba za a samu dan takarar hadin kai ba, inda ya ce ADC za ta gudanar da zaben fidda gwani (primary election) kamar yadda sauran jam’iyyu ke yi.

A bangaren Obi kuwa, rahotanni sun bayyana cewa baya da niyyar fuskantar Atiku a cikin zaben fidda gwani.

“Ba za mu shiga zaben da aka ‘dollarize’ ba” – Kungiyar Obidient

Kungiyar goyon bayan Obi wato Obidient Movement ta ce shugaban su ba zai shiga kowace irin zabe ta delegates da ake amfani da kudi ba.

Dr. Yunusa Tanko, Koodinetan kasa na kungiyar, ya bayyana cewa siyasar Obi ba ta karɓi tsarin “zaben da ake biyan delegates da daloli” ba.

A cewarsa:

“Peter Obi ba zai shiga zaben delegates da ake biya da kudi ba.

Wadannan mutane da suka tara dukiya mai yawa za su iya cin zarafinsa.

Mu muna tafiya da tsarin siyasa daban. Obi ba zai shiga zaben da aka cika da kudi ba.”

Yunusa ya kuma ce tun da shugabancin kasa an ware shi ga kudu, bai kamata a cigaba da maganar dan takarar Arewa ba.

A gefe guda, Atiku ya bayyana cewa ba zai ja da baya don kowa a jam’iyyar ADC ba.

Da aka tambayi ko Obi zai iya sauya sheka zuwa wata jam’iyya, Tanko ya ce:

“Idan muka kai ga wannan matakin, sai mu dauki mataki.”

ADC ta ki yin tsokaci kan batun zaben fidda gwani

Mai magana da yawun jam’iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya ce jam’iyyar bata fara tattaunawa kan wanda zai tsaya mata a zaben 2027 ba.

Ya ce:

“Babu wanda ke tattaunawa yanzu kan dan takarar hadin kai ko zaben fidda gwani.

A yanzu mu na kan kokarin gina jam’iyyarmu, ba tattaunawa kan dan takarar shugaban kasa ba.”

Game da dalilin da yasa Obi bai yi rajista da jam’iyyar ba, Bolaji ya ce:

“Obi da El-Rufai ba su zama mambobi na ADC ba tukuna.

Obi yana son ya tallafa wa ‘yan takarar jam’iyyarsa ta asali kafin ya shiga ADC gaba ɗaya bayan zaben Anambra.”

Lalacewar LP na iya hana Obi tsayawa takara

Wasu masu sharhi sun bayyana cewa Obi ba zai iya amfani da jam’iyyar Labour Party (LP) a 2027 ba saboda rikicin cikin gida da ke damun jam’iyyar.

Masanin siyasa Dr. Anabi Samuel, ya ce rikicin da ke tsakanin Julius Abure da wasu mambobi zai iya hana Obi samun tikitin jam’iyyar.

A cewarsa:

“Peter Obi ya samu abokan gaba a LP.

Ko da ya samu tikiti, wadannan mutanen da ke cikin jam’iyyar za su iya hana shi cin nasara.”

Ya kuma kara da cewa idan Obi bai samu tikitin ADC ba, zai fi kyau ya jinkirta burinsa, sai dai idan PDP ta amince ta bashi tikiti.

LP: Ba za mu bawa Obi tikitin kai tsaye ba

Duk da cewa wasu suna ganin Obi ne ya daukaka LP a siyasar Najeriya, jam’iyyar ta bayyana cewa ba za ta bashi tikitin kai tsaye (automatic ticket) ba.

Mai magana da yawun LP na kasa, Obiora Ifoh, ya ce:

“Zaben fidda gwani zai kasance cikin dimokuradiyya.

Duka mukamai za a bude su domin masu sha’awa su tsaya.

Bai kamata a bawa kowa tikitin kai tsaye ba.”