Close Menu
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp
Twins Empire News
Demo
  • Gida
  • Labarai
  • Wasanni
  • Nishadi
  • Siyasa
  • Bidiyo
  • Game damu
  • Tuntubemu
Twins Empire News
Home»Labarai»Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 30, Yuli. 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 30, Yuli. 2026

By Ahmad Habib IbrahimYuli 30, 2026No Comments3 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Reddit Telegram Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

1. An kama Sakataren Gwamnatin Osun da wasu mutum biyar
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Osun ta tabbatar da kama Sakataren Gwamnatin Jihar, Hon. Teslim Igbalaye, tare da wasu mutum biyar. A yayin samamen da aka kai gidansa, an kwato kuɗi har Naira miliyan 4.81, kwamfuta, na’urar kwafi (photocopier), firinta, katunan zaɓe guda biyu (PVCs) da kuma kundin rajistar masu zaɓe na gundumomi 15.

2. Rundunar Sojin Ƙasa ta naɗa sabbin Kwamandojin Divisions
Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya naɗa sabbin General Officers Commanding (GOCs)domin jagorantar sabbin rundunonin soji da aka kafa, bayan amincewar Shugaba Bola Tinubu, domin ƙarfafa ayyukan tsaro a faɗin ƙasar.

3. ADC ta caccaki Tinubu kan furucin “zan yi yaƙi har ƙarshe”
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta soki Shugaba Bola Tinubu bisa furucinsa cewa a shirye yake ya yi gwagwarmayar siyasa har ƙarshe. Jam’iyyar ta ce maimakon haka ya kamata ya mayar da hankali wajen yaƙar ‘yan ta’adda da matsalar tsaro da ke addabar ƙasar.

4. ‘Yan sanda sun gaza gabatar da shugaban PFIPC a gaban Majalisar Wakilai
Rundunar ‘Yan Sanda ba ta gabatar da Adeyemi Adeniyi, wanda ke ikirarin shi ne Darakta Janar na PFIPC, a gaban kwamitin binciken Majalisar Wakilai ba. Rundunar ta ce tana buƙatar umarnin kotu kafin ta sako shi daga tsare domin gabatar da shi.

5. ‘Yan bindiga sun kashe mutum uku a cikin masallaci a Sokoto
Aƙalla mutum uku sun rasa rayukansu a cikin wani masallaci yayin da ‘yan bindiga suka kai hari ƙauyen Tsamaye da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto. Haka kuma sun yi garkuwa da mutane da dama.

6. An kashe jami’an tsaro huɗu a Kebbi
Jami’an tsaro huɗu sun mutu, yayin da wani soja ya ɓace bayan harin da aka kai ƙauyen Tudun Bicci a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi.

7. DSS ta gurfanar da wasu da ake zargi da kasancewa mambobin Ansaru
Hukumar Tsaro ta DSS ta gurfanar da wasu mutum biyar da ake zargin mambobi ne na ƙungiyar Ansaru a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja. Ana zarginsu da hannu a sace ɗalibai da malamai a Jihar Oyo tare da kashe wasu mutum biyu.

8. INEC ta ƙara wa’adin karɓar katin zaɓe a Osun
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tsawaita lokacin karɓar Katin Zaɓe (PVC) har zuwa 31 ga Yuli, domin shirye-shiryen zaɓen gwamnan Jihar Osun na ranar 15 ga Agusta, 2026. Hukumar ta tabbatar da cewa ƙuri’u ne za su tantance sakamakon zaɓen, ba tashin hankali ba.

9. Masu yaƙin neman zaɓen Adeleke sun nemi a saki magoya bayansu
Tawagar yakin neman zaɓen Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ta buƙaci a saki magoya bayanta da aka kama. Ta zargi rundunar ‘yan sanda da kama sama da mutum 86 ba tare da hujjar doka ba.

10. Peller da Jarvis sun yi auren kotu
Fitattun masu ƙirƙirar bidiyo a TikTok, Hamzat Habeeb Adelaja (Peller) da Amadou Elizabeth Aminata (Jarvis), sun yi auren kotu (Civil Wedding) a ranar Laraba. Wannan na daga cikin shirye-shiryen aurensu na farin kaya da aka tsara yi a ranar 1 ga Agusta, 2026.

Labaran Safiyar Yau
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Ahmad Habib Ibrahim
  • Website

Related Posts

Dangote: Najeriya na iya fara sayen fetur da dizal da dalar Amurka – PETROAN

Yuli 20, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 16, Yuli. 2026

Yuli 16, 2026

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 15, Yuli. 2026

Yuli 15, 2026

Comments are closed.

Twins Empire Youtube
Wallafar Yanzu
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 30, Yuli. 2026
  • “Idan Wani aAbu Ya Sami El-Rufai, SakamakonsaZai Zama Abin Da Ba Za A Iya Hasashe Ba” – ADC ta gargadi Tinubu
  • Dangote: Najeriya na iya fara sayen fetur da dizal da dalar Amurka – PETROAN
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 16, Yuli. 2026
  • Takaitattun Labaran Safiyar Yau Laraba 15, Yuli. 2026
Nasara
Tsari
© 2026. Designed by Syntape Soultions.
  • Labarai
  • Nishadi
  • Wasanni
  • Contact Us

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.