Labaran Najeriya Na Yau – 28 Ga Oct, 2025
1. Shugaba Tinubu Ya Sadu Da Sabbin Hafsoshin Tsaro:
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da sabbin hafsoshin tsaro a fadar gwamnati, Abuja, a ranar Litinin. Wannan ganawa ce ta farko tun bayan nada su kwanaki uku da suka gabata, kuma an gudanar da ita a bayan ƙofa.
2. Nnamdi Kanu Ya Fasa Kiran Shaidu A Kotu:
Shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya sanar wa kotu cewa ya janye shirin kiran shaidu domin kare kansa, yana mai cewa babu wani hujja da ke tabbatar da laifin da ake tuhumar sa da shi.
3. APC Ta Gargadi Jama’a Su Riƙe Gwamnoni Da Shugabannin Kananan Hukumomi Accountable:
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce yanzu gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi suna karɓar kuɗin da ya ninka sau uku zuwa hudu fiye da da, don haka ya kamata ‘yan Najeriya su tambaye su yadda ake kashe kudin.
4. Kabiru Tanimu Turaki Ya Mika Takardun Neman Kujerar Shugaban PDP:
Tsohon Ministan Harkokin Musamman, Kabiru Tanimu Turaki, SAN, ya mika takardun neman kujerar shugaban jam’iyyar PDP. Za a gudanar da babban taron zaben shugabanni na jam’iyyar a ranar 15–16 ga Nuwamba, 2025 a Ibadan, Jihar Oyo.
5. Gwamna Oyebanji Ya Lashe Tikitin APC Na Zabe Na Biyu:
Gwamnan Jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji, ya samu tikitin jam’iyyar APC domin neman wa’adin mulki na biyu ta hanyar matsayar hadin kai (consensus) a zaben fidda gwani da aka gudanar a Ado-Ekiti ranar Litinin.
6. Shugaban INEC Ya Yi Alkawarin Gyara Tsarin Shari’o’in Zabe:
Sabon shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce zai kawo karshen yawan shari’o’in da ake yi kafin zabe. Ya bayyana haka ne a taron shekara-shekara na ƙungiyar malamai masu koyar da dokoki a jami’ar Abuja.
7. Ma’aikatar Shari’a Ta Kare Shari’ar Da Ta Kai Kan Sanata Natasha:
Ofishin Babban Lauyan Kasa ya bayyana cewa karar da aka kai kan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan saboda batanci da kalaman da ta yi kan shugaban majalisa Godswill Akpabio da tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello na bisa doka.
8. Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga ’Yan Fashi Uku A Ekiti:
Babbar kotu a Ado-Ekiti ta yanke hukuncin kisa ta rataya ga mutum uku bisa laifin fashi da makami da suka aikata a gidan wata tsohuwa mai shekara 87, inda suka kwace mata N186,000 da agogo.
9. ‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Mai Ajiye Kuɗi Kwanton Bauna A Ibadan:
‘Yan bindiga sun farmaki wani mutum da ya fito daga banki a yankin Osuntokun, Ibadan, inda suka jikkata ɗan sanda kuma suka kwace masa kuɗin da bai bayyana adadinsa ba.
10. Paul Biya Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Kamaru:
Kotun kundin tsarin mulki ta Kamaru ta bayyana Paul Biya, mai shekaru 92, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa. Biya, wanda yake mulki tun 1982, ya samu kashi 53.66 cikin dari na kuri’un da aka kada.

