Labaran Najeriya Na Yau – 2 Ga Satumba, 2025
1. Kotun Finland ta yanke wa Simon Ekpa hukuncin shekaru 6 a kurkuku
Kotun yankin Päijät-Häme a Finland ta same shi da laifin ta’addanci, ta kuma yanke masa hukunci daurin shekaru shida.
2. ONSA ta karyata ikirarin El-Rufai kan biyan kudin fansa ga ‘yan ta’adda
Ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro ya ce wannan magana karya ce kuma babu hujja akanta.
3. Gwamnatin tarayya ta ce za a gyara layin dogo na Abuja-Kaduna cikin kwanaki 10
Ministan Sufuri, Said Ahmed Alkali, ya tabbatar da hakan bayan hatsarin jirgin kasa a Asham Station.
4. ‘Yan daba sun kai hari kan rakiyar tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami
Lamarin ya faru ne kusa da gidan Malami a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi.
5. Bayo Onanuga: Masu kiran a sauke Tinubu ‘yan siyasa ne masu son mulki
Ya ce kalaman El-Rufai da cewa Tinubu ba zai yi nasara ba a 2027 siyasa ce kawai.
6. ‘Yan sanda sun kama dalibai 7 da ake zargi da zama ‘yan kungiyar asiri a Akwa Ibom
An same su da ƙashi da kuma bindiga bayan bayanan sirri daga tsohon mamba.
7. Sanata Kabiru Marafa ya yi barazanar cire kuri’u miliyan 1 daga Tinubu a 2027
Ya zargi shugaban ƙasa da siyasar “a yi amfani a watsar.”
8. Likitocin NARD sun bai wa gwamnati wa’adin kwana 10
Kungiyar ta ce za ta shiga yajin aiki idan ba a biya musu bukatun alawus da walwala ba kafin wa’adin ya kare.
9. ASUU ta yi gargadi cewa gwamnati ke da alhakin yuwuwar sake rufe jami’o’i
Kungiyar ta zargi gwamnati da tura malaman jami’a zuwa yajin aiki ta gangan.
10. Ibok-Ete Ibas ya rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi a Rivers
Ya ja kunnen su su mayar da hankali kan ci gaban al’umma a matakin tushe.