Tel Aviv, Isra’ila —
Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila na tattaunawa da Kudancin Sudan kan yiwuwar karɓar Falasdinawa daga zirin Gaza domin sake tsugunar da su a ƙasar, wanda har yanzu ke fama da yaƙi da talauci.
Mutane shida da suka san da lamarin sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa an fara tattaunawa, duk da cewa ba a fayyace matakin da aka kai ba. Idan aka aiwatar, wannan shirin zai iya zama kamar mayar da jama’a daga wuri mai fama da yaƙi da yunwa zuwa wani wuri mai irin wannan matsala, lamarin da ya jawo ƙarar naƙasu daga kungiyoyin kare haƙƙin bil’adama.
Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce yana son ganin an aiwatar da hangen nesa na Shugaban Amurka Donald Trump na “ƙaura da yardar rai” daga Gaza. Sai dai ƙasashen duniya da dama, ciki har da Masar, sun nuna adawa, suna mai cewa hakan na iya zama tilasta wa Falasdinawa barin ƙasarsu.
Ma’aikatar harkokin wajen Kudancin Sudan ta musanta rahotannin da ke cewa tana shirin karɓar Falasdinawa, tana mai cewa “ba wannan ne matsayar gwamnatin ƙasar ba.” Duk da haka, wasu jami’an ƙasar sun tabbatar da tattaunawa a ɓoye.
Masar ta bayyana adawa da shirin, tana mai fargabar cewa hakan zai ƙara ƙaurar ‘yan gudun hijira zuwa yankinta da ke makwabtaka da Gaza.
Kudancin Sudan, wanda ya fito daga dogon yaƙin basasa bayan samun ‘yanci a shekarar 2011, na ci gaba da fama da rikice-rikice, talauci da yunwa, inda sama da mutane miliyan 11 ke bukatar tallafin abinci.
Kungiyoyin farar hula a ƙasar sun gargadi gwamnati da ta guji zama “ɗakin ajiyar mutane,” tare da nuna cewa Falasdinawa na iya fuskantar ƙalubale saboda tarihin rikici tsakanin Arewa da Kudu kafin ƙasar ta balle daga Sudan.