Site icon TWINS EMPIRE

Gwamnatin Kano Tana Gudanar Da Bincike

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci a gudanar da cikakken bincike kan zargin da Kwamishinan Harkokin Sufuri, Alhaji Ibrahim Namadi, ya bayar da beli ga Sulaiman Aminu Danwawu, wanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi. Wannan matakin ya biyo bayan fushin jama’a da aka samu bayan ganin sunan kwamishinan a jikin takardun belin wanda ake zargi.

Gwamna ya sanar da kafa kwamitin bincike na musamman, wanda zai binciki lamarin da bayar da shawarar daukar mataki. Kwamitin yana karkashin jagorancin Barrista Aminu Hussain, mai ba Gwamna shawara kan harkokin Shari’a da Dokoki, tare da mambobi da dama ciki har da Barr. Hamza Haladu da Manjo Janar Sani Muhammad (Rtd.).

Gwamna Yusuf ya bayyana damuwarsa kan wannan lamarin, kuma ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci ayyukan laifi ko tallafa wa rashin ɗa’a ba.

Exit mobile version