“Zan iya cewa mutumin da na hadu dashi ako da yaushe yake tunamin da Khalifa Umar Bn Abdul’aziz shi ne Alh Ahmad Idrsi (Akanta Janar)” – Nasir NID

Wanene Akanta Janar?Na taba karanta tarihin Khalifa Umar Bin Abdul’aziz, wanda ya mulki daular Musulunci a shekaru 88 bayan wafatin Annabi (SAW) a matsayinsa na shugaba daula, ya zama mai karanci mai tausayi mai taimakon marasa karfi, mai saukin kai da haba haba da jama’a, hakanan wanda ako da yaushe yake yiwa al’umma hidima da kansa, ta yadda har duniyar Musulunci ta yi Ittifaqin cewa shine cikamakin Khulafa’ur Rashida saboda adalcinsa.Na hadu da wasu daga cikin shugabannin da masu rike da madafun iko da dama, amma zan iya cewa mutumin da na hadu dashi ako da yaushe yake tunamin da Khalifa Umar Bn Abdul’aziz shine Alh Ahmad Idrsi (Akanta Janar).

Wata rana na raka wani abokina gidansa sai na tarar da gidan cike da mutane, sai na hangi wani mutum ya na zubawa mutane abinci, sai abokin nawa yace wancan fa shine Akanta Janar, nayi mamakin saukin kansa. Bayan ya gama zubawa mutane abinci, sai ya karaso inda muke, muka gaisa, sai ya ce ku zo muci abinci, ya je ya zubo mana abinci a filet mukaci tare.Na hadu dashi ba sau daya ba ba sau biyu ba, ako da yaushe sai ya yi mana hidima, kamar ba shugaba ba. Ya taba ganina ina mura, sai ya ce zaifi kyau ka sha shayi, sai na ce to, sai ya mike tsaye ya ce mu shiga tuarakarsa, da kansa ya dafa shayi ya bani, wannan abu ya bani mamaki.Wanda ya sanshi zai fada maka cewa, baya gajiya da taimakon al’umma.

Ko a Musulunci Malamai sun fada mana cewa, abinda ake so ga Bawa aiyukan alkairin mutum suka rinjayi sharrinsa. Akwai aiyukan alkairinsa bila adadin da na sani, ba kawai Masallatai da makaratun da asibiti da rijiyoyin burtsaye daya samar da kudinsa ba, ya dauki nauyin karatun ‘ya’yan talakawa a ciki da wajen kasar nan, ni ban taba ganin mutum mai karamcin ba.Idan kuna magana dashi, zai fada muku cewa, idan kuka samu dama ku taimaki marasa karfi, kuma ku rike amana ku ji tsoron haduwarku da Allah.

Na koyi abubuwa da dama daga rayuwarsu.Wata rana wani mutum ya taba fada min cewa a tarihin Kano, ba a taba samun mutumin da ya samowa ‘yayan talakawa aiki kamarsa ba, ko da yaushe gidansa cike yake da matasa rike da CV da suke so su hadu dashi domin ya sama musu aiki, idan yana gari sai ka rantse da Allah daurin aure ake yi a gidansa saboda yawan mutanen dake son ganinsa. Na tuna wata magana da ya taba fada a gabana yace, idan kana aikin alkairi, kada ka taba damuwa da duk wani sharri da kage da bita da kullin da za a yi maka, kai dai ka rike amana, kuma ka taimaki Jama’a Allah baya barci, kuma ya fika sanin kanka..Ban ce ba zai iya yin kuskuke ba, amma a yadda na sanshi nayi Imanin cewa zargin da hukumar EFCC take yi masa baiyi kama da gaskiya ba, kuma na tabbata aiyukan alkairi da kyawawan dabi’unsa na tausayi da jin kai da gaskiyarsa za su fitar da shi. Allah baya juyawa masu gaskiya baya.

Daga Nasir Nid