Zan ƙalubalanci Tinubu a takarar shugaban ƙasa – Sanata Orji Kalu

Tsohon Gwamnan Jihar Abia kuma Sanata a Majalisar Dattijan Najeriya Orji Kalu ya ce ya shirya tsaf don yin takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar.
Da yake magana da manema labarai ranar Talata, Sanata Kalu ya ce ya yi imanin “lokaci ya yi da yankin kudu maso gabas zai samar da shugaban ƙasa”.
Ya ƙara da cewa zai ƙalubalanci Bola Ahmed Tinubu, Bayerabe kuma ɗan yankin kudu maso yamma wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar, idan APC ta amince ta bai wa yankin Kudu takarar.
“Ba na kallon takarar Tinubu a matsayin wani cikas game da yunƙurin ƙabilar Igbo na samar da shugaban ƙasa,” in ji Mista Kalu. “Saboda muna magana ne kan makomar Najeriya.
“Obasanjo ya yi shugaban ƙasa tsawon shekara takwas, Yemi Osinbajo na yin mataimakin shugaban ƙasa shekara takwas, amma babu wani ƙabilar Igbo da aka zaɓa a matsayin shugaban ƙasa tun bayan samun ‘yancin kai.
“Saboda haka yana da kyau a kodayaushe a dinga tunani kan abin da ya kamata a yi da kuma wanda ya fi dacewa.”
Shi ma Gwamnan Ebonyi David Umahi\, daga kudu maso gabas, ya bayyana cewa ya faɗa wa Shugaba Muhammadu Buhari sha’awarsa ta tsayawa takarar a APC.