Za’a cigaba da amfani da tsohuwar N200

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa babban bankin ƙasar umurnin ya sake fito da tsofaffin takardun naira 200 domin a ci gaba da mu’amala da su a ƙasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya yi wa al’ummar ƙasar da safiyar yau Alhamis.

Buhari, wanda ya ce yana sane da irin halin wahala da al’ummar ƙasar ke ciki, ya ce za a ci gaba da amfani da takardar kuɗin ta naira 200 har zuwa 10 ga watan Afrilu.

Ya kuma buƙaci al’umma da su ƙara haƙuri kan halin da ake ciki.