Za mu taimaka wa masu son mallakar makami don kare kansu – Gwamna Masari
Gwamnan Katsina Aminu Masari ya nemi mazauna jiharsa da su sayi makamai don su kare kan su daga hare-haren ‘yan fashin daji da ke addabar yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Da yake tattaunawa da ‘yan jarida ranar Talata a fadar gwamnatin Katsina, Masari ya ce ‘yan sandan da ke jiharsa ba su kai 3,000 ba, yana mai cewa gwamnati za ta taimaka wa masu son mallakar makaman don taimaka wa harkar tsaro.
“Harkar tsaron nan ta kowa da kowa ce babu bambancin siyasa…abin da mutane ya kamata su sani shi ne a Katsina ba ka da ‘yan sanda 3,000…saboda haka muke kira ga duk wanda zai iya ya nemi makami ya kare kan sa da iyalansa,” a cewar gwamnan.
Ya ci gaba da cewa: “Shari’ar Musulunci ma ta yarda mutum ya kare kan sa da dukiyarsa da iyalansa. Idan ka mutu kana ƙoƙarin kare kanka ka yi shahada. Abin baƙin ciki ma shi ne ta yaya ‘yan fashi za su samu bindiga amma mutanen kirki ba su da ita da za su kare kansu da iyalansu.”
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta taimaki duk wanda yake son ya mallaki makami don daƙile ayyukan ‘yan fashi. “Za mu taimaki waɗanda ke son shigo da makamai saboda akwai buƙatar ‘yan Katsina su taimaka wa jami’an tsaro.”
Sai dai gwamnan ya soki ayyukan ‘yan sa-kai (‘yan banga), yana mai cewa “ba mu yarda da aikin ‘yan sa-kai ba saboda ƙaura suke yi daga garinsu zuwa wani gari, mun fi son mutane su kare garuruwansu da kansu”.