Za mu dawo da kundin tsarin mulki a lokacin da ya dace – Paul-Henri Damiba
Sabon shugaban mulkin soja na Burkina Faso, Laftanar Kanar Paul-Henri Damiba, ya yi jawabi a karon farko tun bayan hawansa mulki a ranar Litinin.

Da yake jawabi sanye da jajayen kayan soji, Kanal Damiba ya yi alkawarin komawa kan tsarin mulkin kasar da aka saba cikin abin da ya kira “lokacin da ya dace”.
Ya ce zai kira taron wakilan bangarori daban-daban na al’ummar Burkina Faso domin cimma matsaya kan tasawirar kawo sauyi.
“Na fahimci shakku mai ma’ana da wasu daga cikinku ke nunawa game da sauyin da aka samu a tsarin tafiyar da mulkin wannan ƙasa, amma ina son tabbatar wa kawayen Burkina Faso cewa za mu ci gaba da mutunta dokar kasa da kare hakkin dan Adam,” a cewarsa.
Kanar Damiba ne ya jagoranci sojojin da suka kifar da Shugaban Ƙasa Roch Marc Kabore daga kan karagar mulki, yana mai zargin sa da gazawa wajen dakile tashe-tashen hankal na masu ikirarin jihadi.