Za a tilasta wa ma’aikatan gwamnatin Najeriya yin allurar riga-kafin korona

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za ta tilasta wa duk wani ma’aikacinta karɓar allurar rigakafin korona.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a Abuja.

Mista Mustapha ya ce duk da cewa a yanzu gwamnati ba ta da isasshiyar allurar rigakafin, hakan ba zai hana ta wajabta wa duk wani ma’aikaci yinta ba.

Ya kara da cewa ana ci gaba da kokari wajen ganin an daƙile yaɗuwar annobar da kare ‘yan kasa baki ɗaya.

A watan da ya gabata ne mahukuntan ƙasar suka yi gargaɗin cewa Najeriya ta fara shiga mataki na uku na annobar korona, har ma an samu kimanin mutum goma da suka kamu da sabon nau’in annobar mai suna Delta.

Sai dai sun ce ana ci gaba da bin dukkan matakan da suka kamata don ganin an daƙile yaɗuwarta.