Za a samu ɗaukewar wutar lantarki a sassan Abuja ranar Asabar

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC) ya sanar da cewa za a samu ɗaukewar lantarkin na tsawon awa bakwai a wasu sassan Abuja babban birnin Najeriya gobe Asabar sakamakon matsalar da tashar lantarki ta Apo ta samu.

Wata sanarwa da kamfanin ya fitar a yau Juma’a ta ce za a samu matsalar wutar ce daga ƙarfe 9:00 zuwa 4:00 na yamma.

Sanarwar ta kara da cewa rashin wutar da ake fama da shi a yanzu na faruwa ne sakamakon ƙarancin wutar da ake samu daga kamfanin tattara wutar wato Generation Companies (GenCos) yayin da kamfanonin ke ƙoƙarin matsalar. 

Yankunan da lamarin zai shafa sun hada su ne: Lokogoma, Apo Machanic Village, Apo Resettlement, Waru Village, Gaduwa Estate, Trademore Estate, Apo Legislative Quaters, Behind Transmission Substation, Efab Galaxy Estate, Efab Sunshine Estate, CedaCrest Hospital da kuma kewaye.

Za’a katse wutar ne don bai wa kamfanin (TCN) damar duba wasu taransifomomi da ke tashar ta Apo.