Najeriya na fuskantar matsananciyar yunwa, inda kimanin mutane miliyan 31 ke cikin hadarin rashin abinci mai gina jiki, musamman a yankunan Arewa maso Gabas da wasu sassan Arewa ta Tsakiya.
Hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) da sauran kungiyoyi sun yi gargadin cewa rashin kudade da tabarbarewar tsaro na iya tilasta rufe cibiyoyin kula da abinci guda 150 a jihar Borno. Wannan zai shafi dubban mata da kananan yara da ke dogaro da wadannan cibiyoyi don samun abinci da kulawa.
Matsalar ta samo asali daga hare-haren ‘yan ta’adda, tashe-tashen hankula, da kuma canjin yanayi, wanda ya rage yawan amfanin gona da samun ruwa. Kungiyoyin agaji na neman karin tallafi daga gwamnati da al’umma don dakile barkewar karancin abinci.