Yunusa Yellow Ya Shaki Iskan Yanci

A Safiyar Yau ne dai Yunusa Yellow ya Shakin iskan yancin bayan shekarun da ya shafe a tsare

A shekarar da ta gaba ta ne dai Kotun daukaka kara ta Fatakwal ta rage hukuncin daurin shekaru 26 da wata babbar kotun tarayya da ke zama a Yenagoa ta jihar Bayelsa ta yankewa Yunusa Dahiru a watan Mayun 2020.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa Mai shari’a Jane Inyang ta yankewa Mista Dahiru, wanda aka fi sani da Yellow hukuncin daurin shekaru 26 a gidan yari bisa samunsa da laifin safarar yara da kuma lalata da wani matashi Ese Oruru.

Da rashin gamsuwa da hukuncin da kotun ta yanke, Mista Dahiru ya daukaka kara, inda ya nemi a wanke shi.

Sai dai a safiyar yau Yunusa Yellow ya kammala wa’adin da aka deban masa a katun.