Yunkurin Burtaniya na tura masu neman mafaka Rwanda na fuskantar cikas
Yunkurin tura masu neman mafaka daga Burtaniya zuwa Rwanda na fuskantar cikas, bayan ƙalubalantar matakin a kotun kare haƙƙin ɗan adam ta Tarayyar Turai.
Kotun da ke Strasbourg ta bayar da umarni da ya hana korar ɗaya daga cikin mutanen da za su shiga jirgi a tafi da su.
Ofishin harkokin cikin gida a Landan yana tunanin cewa kotu za ta iya hana shirin korar mutanen da aka yi a yau.
Tun da farko Firaministan Boris Johnson ya nace kan aniyarsa ta aiwatar da manufar da ke fuskantar suka, amma a cewarsa mataki ne na daƙile aikin masu safarar mutane.