‘Yan sanda sun kama matar da ta cina wa budurwar mijinta wuta ta rasu
‘Yan sandan jihar Ogun sun kama matar aure Kehinde Abdulwasiu mai shekara 32 da laifin cina wa budurwar mijinta Tosin Olugbade mai shekara 23 wuta.
Kakakin rundunar Abimbola Oyeyemi ya sanar da haka wa manema labarai a garin Abeokuta a farkon wannan makon.
Ya ce rundunar ta kama Kehinde bayan mijin Tosin, Fatai Olugbade ya kawo kara ranar 22 ga Nuwamba.
“Olugbade ya ce wata rana daga kawai ya zargi Tosin da neman maza shine Tosin ta tattara kayan ta ta tare gidan Ismail Wasiu wato saurayinta Kuma mijin Kehinde.
“Ina zaune a gida sai na samu labarin cewa Tosin ta yi fada da matar Wasiu, Kehinde inda cikin fushi Kehinde ta duldula mata fetur ta kesta ashana.
“Tosin ta rasu a asibiti a lokacin da ake duba ta a asibiti.
Oyeyemi ya ce ‘yan sanda sun kama Wasiu saboda Kehinde ta gudu.
“Da yake tsare a ofishin mu Wasiu ya ce Tosin ta rasu a dalilin fashewar tukunyar gas din da take girki da shi.
Ya ce binciken da rundunar ta gudanar ya nuna cewa karya Wasiu ya yi sannan shine ya ce wa matarsa Kehinde ta gudu.
Oyeyemi ya ce rundunar ta kama Kehinde a Saki jihar Oyo.
Ya ce fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka za ta ci gaba da gudanar da bincike