‘Yan sanda sun ceto mutum 20 da shanu da dama a jihar Neja

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan banga sun ceto mutum 20 da shanu da dama daga ‘yan bindiga a kauyen Nasko dake karamar hukumar Magama.

Kakakin rundunar Wasiu Abiodun ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai ranar Litini.

Abiodun ya ce rundunar ta kashe ‘yan bindiga da dama a arangamar da suka yi da ‘yan bindigan a kauyen.

“A ranar 12 ga Faburairu 2022 jami’an tsaro sun yi barin wutan da ‘yan bindigan da suka afka kauyen Nasko inda suka ceci mutum 20 da shannu da dama da ‘yan bindigan suka sace daga kauyen.

“Jami’an tsaron sun kwato bindiga kirar AK47 guda daya da harsashi 30 a cikin bindigan, wayar salula 7 da babur Kiran Honda guda daya.

Bayan haka a ranar 13 ga Janairu 2022 jami’an tsaro sun gano mabuyar ‘yan bindiga a kan dutsen Anaba dake karamar hukumar Magama.

Jami’an tsaron sun kwato babban bindiga kirar AK-47 da harsashi 13 a ciki da aka boye a tsakanin wasu duwatsu.

Abiodun ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Monday Kuryas ya jinjina kokarin da jami’an tsaron suka yi sannan ya hore su da su kara zage damtse domin ganin an kawo karshen ayyukkan ‘yan bindiga a jihar.