‘Yan sanda sun ce mutum huɗu sun mutu a fashewar tulun gas a Sabon Gari a Kano

Rahotanni daga jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya na cewa wani abu ya fashe a Aba Road da ke Unguwar Sabon Gari a birnin Kanon.

Lamarin ya rutsa da mutane da dama ciki har da yara ƴan makaranta.

“Rufin makarantar ya yaye saboda ƙarfin fashewar tukunyar gas ɗin. Dukkan hanyoyin da suke kusa da wajen sun cika maƙil da jama’a waɗanda ke ciki da damuwa da alhini, inji shaidun gani da ido

Tuni kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano CP Sama’ila Dikko da shugaban hukumar DSS na jihar sun halarci wajen, sannan motocin asibiti sun je don kwasar waɗanda harin ya rutsa da su.

BBC ta ruwaito cela CP Dikko ya shaida mata cewa tulun gas da ake walda da shi a wajen ne ya fashe, “amma ba bam ne ya tashi ba kamar yadda ake faɗa,” in ji kwamishinan.

Ya ƙara da cewa an gano gawarwaki huɗu kuma ana ci gaba da bincike. Amma ana iya ganin jini ta ko ina a wajen da kuma wasu sassan jikin mutane.

Jami’an tsaro sun yi ta ƙoƙarin shawo kan mutane waɗanda da alama ke fusace, don su bari a yi bincike kan musabbabin faruwar lamarin.

An daɗe ba a ji labari mai kama da wannan ba wato na kai harin bam a jihar Kanon, dalilin da ya sa hakan zai jefa mutane cikin ruɗanin wa yake da alhakin hakan.

Ba a Kano kaɗai ba, an samu sauƙin tashin bam a faɗin Najeriya a shekarun bayan nan, ba kamar a da ba da hakan ya zama kusan ruwan dare.