‘Yan Najeriya Na Ci Gaba Da Korafi Kan Yadda Ake Yiwa Jama’ar Kasar Kissan Kiyashi

A Najeriya jama’a na ci gaba da yin tofin Allah tsine akan yadda mahukumta ke zura idanu ana yiwa jama’ar kasar kissan kiyashi, a daidai lokacin da ake ci gaba da alhinin kisan gilla da ‘yan bindiga suka yiwa matafiya da hukuma ta tabbatar da adadinsu ya kai 23. 

Jihohin arewacin Najeriya musamman na Arewa maso yamma na ci gaba da fuskantar munanan hare-haren ta’addanci wadanda kuma ke haddasa asarar rayukan jama’a da dukiyoyi.

Na baya-bayan nan mafi muni shine wanda aka kona matafiya 23 a jihar Sakkwato wanda ya sa jama’ar yankunan ke tunanin ko wani shiri aka kula da don a karar da jama’ar.

Wannan lamarin dai ya janyo hankalin kungiyoyi da hukumomi a duniya na kira ga gwamnatin Najeriya akan daukar matakan shawo kan matsalolin rashin tsaro kamar kungiyar mabiya addinin kirista ta Najeriya wadda tayi Allah wadai da wannan aika-aikar har take ganin cewa yanzu a Najeriya rayuwar dan tsako tafi ta bil’adama daraja, kammar yadda mataimakin shugaban kungiyar mai kula da Jihohin arewa da Abuja Rev John Joseph Hayab ya bayani wanda jaridar Vanguard ta wallafa.

To amma bayan faruwar wannan lamarin kwamishinan ‘yan sanda a jihar Sakkwato Kamaluddeen kola Okunlola yace jami’an tsaro sun matsa kaimi ga sintirin hanyoyin dake yankin.

“Tun daga wannan lokacin ana ci gaba da sintirin wannan hanyar har zuwa shinkafi don dakile ayukkan ‘yan bindigar, kuma ana ci gaba da daukar matakan kare sake faruwar hakan.”

Jama’a dai na ganin kamar da gan-gan gwamnatin Najeriya ta kyale wani bangare na kasar na shan ukuba, inji farfesa Bello badah.

Wasu rahotanni na nuna cewa duk da sintirin da kwamishinan ‘yan sanda ya ce ana yi akan hanyar Isa zuwa Shinkafi an sake kai hari cikin daren jiya alhamis akan wata motar matafiya dake dawowa daga kasuwar shinkafi kamar yadda wani mazaunin yankin Isa ya sheda wa muryar Amurka.