‘Yan Kasuwar Shanu A Aba Na Neman Wasu Mutanensu Da Suka Bata

Hakan na faruwa ne yayin da rahotanni ke nuna cewa an halaka wasu mutum biyu da ke sanaa’r sayar da nama a jihar Anambra. 

Masu sana’ar dabbobi a garin Aba da ke jihar Abia a kudu maso gabashin Najeriya, na ci gaba da neman wasu daga cikin abokanan sana’arsu da suka bata a lokacin wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a kasuwarsu.

A makon da ya gabata ne ‘yan bindigar da ake zargin mayakan IPOB ne suka far wa kasuwar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum takwas. Tuni an yi jana’izarsu a cewar rahotanni.

Wakilin Muryar Muryar Amurka Lamido Abubakar Sokoto ya ruwaito cewa, masu sana’ar dabbobin har yanzu suna cikin yanayi na zama cikin zullumi.

“Gaskiya matakan da aka dauka ba mu gamsu da su ba, saboda yawancin jami’an da aka kawo mana, sun yi kadan.” In ji Muhammadu Sani Jos.

Hukumomin jihar sun yi ikirarin tura jami’an tsaro a kasuwar don su ba ‘yan kasuwar kariya.

Hakan na faruwa ne yayin da rahotanni ke nuna cewa an halaka wasu mutum biyu da ke sanaa’r sayar da nama a jihar Anambra da ke makwabtaka da jihar ta Abia.

Alhaji Musa Sa’idu, Shugaban ‘yan arewa a yankin kudu maso gabas, ya kara da cewa

Ita dai kungiyar ta IPOB ta musanta harin da aka kai a kasuwar shanun, yana mai cewa sam ba su da hannu a hare-haren.

“Don me IPOB za ta kai hari kan ‘yan kasuwar, ai tare muke zama da su, dukkan hare-haren da ake kai wa ba IPOB ke kai shi, mene ne zai sa IPOB ta kai hari kasuwa? musamman ‘yan arewa Hausawa, ‘yan siyasa ne kawai suke abin da suka ga dama.” In ji kakain IPOB, Mr. Chinanzo Nwackukwu.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce kura ta lafa, kuma an umarci mutane da su koma bakin kasuwancinsu, suna masu cewa s shirye suke su ba su kariya, kamar yadda kakain DSP J. Ogbonna ya tabbatarwa Muryar Amurka.