‘Yan daba na tsoratar da ‘yan kasuwa a tsibirin Legas.
Gabanin zanga-zangar adawa da rashin shugabanci na gari da za a fara a ranar 1 ga watan Agusta, wani faifan bidiyo da ya shafi ‘Yan daba na tsoratar da ‘yan kasuwa a tsibirin Legas.

Hotunan da aka rika yadawa, sun nuna yadda ‘yan barandan ke zagayawa a cikin kasuwar tare da yin barazana ga ‘yan kasuwar da mummunan sakamako idan suka ki biyan bukatarsu.
An ji daya daga cikin mutanen da ke cikin faifan bidiyon yana gargadin cewa, “’Yan Najeriya, ba ku kadai ne ke fama da yunwa ba. Kada ku fito a ranar 1 ga Agusta don yin zanga-zangar. To, idan ka samu hankalinka ya fito, ka ga abin da zai same ka.”
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu kiraye-kirayen gwamnati, da malaman addini, da kungiyoyin farar hula suka yi na a hana zanga-zangar da ake sa ran za ta yi.