‘Yan bindigar Da Suka Sace Dalibai A Nasarawa Sun Nemi A Biya Su Naira Miliyan 25

Rahotanni daga jihar Nasarawa sun yi nuni da cewa maharan da ake zargin ‘yan bindiga ne da suka sace mutane 4 a jami’ar gwamnatin tarayya da ke Mararrabar Akunza sun tuntubi iyalansu tare da neman naira miliyan 25 a matsayin kudin fansa.

Majiyoyi daga yankin Mararrabar Akunza dai sun bayana cewa da misalin karfe 11 da rabi na daren ranar Asabar ne masu garkuwa da mutanen suka kira iyalan mutanen 4 tare da mika bukatar a biya su kudin fansa naira militant 25.

A ranar asabar da misaling karfe 8 na dare ne wasu mahara da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai farmaki kan jami’ar ta gwamnatin tarayya dake garin mararabar akunza a babban birnin jihar Nasarawa wato Lafiya, inda suka sace mutane hudu da ake kyautata zaton cewa duk dalibai ne.

Rahotanni daga jihar dai sun yi nuni da cewa lamarin ya auku ne a yayin da ake tafka ruwan sama kama da bakin kwarya.

Haka kuma wani ganau da ya bukaci a sakaya sunana daga yankin da lamarin ya faru ya ce, a yayin harin ‘yan bindigar sun yi ruwan albarusai sama kafin suka yi awon gaba da mutanen hudu zuwa gurin da ba a kai ga tantancewa ba.

Da aka tuntubi kakakin jami’ar ta Mararrabar Akunza, ya musanta cewa mutanen da aka sace daliban jami’ar ne kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito.

A nasa bangare, kakakin ’yan sandan Jihar Nassarawa, ASP Nansel Ramhan ya ce ba bu wanda ya tuntube su daga jami’ar da korafi kan aukuwaír lamarin a hukumance a lokacin hada wannan labarin.

To sai dai ya ce bayan samun labarin da suka yi a kafaffen sadarwa, yan sanda a jihar sun dukufa wajen kubutar da mutanen da lamarin ya rutsa da su.