Yan Bindiga Sun Sace Mutane ’87’ A Sabon Harin Kaduna
Akalla mutanen kauye 87 ne aka yi garkuwa da su a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a wasu kauyukan Kaduna guda biyu na Gangere da Aguna da ke karkashin gundumar Kufana ta karamar hukumar Kajuru.
Aminiya ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin.
Cikakkun bayanai game da lamarin ya kasance cikin zayyana amma an kai wadanda abin ya shafa zuwa inda ba a san inda suke ba.
Wani shugaban yankin kuma shugaban matasa, Ben Yuhana, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, “’yan bindiga sun shiga kauyukan Gangere da Aguba da ke gundumar Kufana ta karamar hukumar Kufana Chiefdom Kajuru inda suka yi garkuwa da mutane 87 a tsakanin daren jiya zuwa safiyar yau. Zan ci gaba da sabunta ku.”
Har yanzu dai gwamnatin jihar ba ta bayar da wata sanarwa a hukumance ba game da lamarin yayin da kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ya kasa mayar da martani kan sakon da aka aike masa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya ce zai koma bayan samun cikakken bayani amma bai yi haka ba har zuwa lokacin da aka gabatar da wannan rahoto.