‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 17 A Neja

‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 17 A Neja

Wasu ‘yan bindiga, a wasu hare-hare guda biyu a jiya Talata, sun yi garkuwa da wasu mutane 17 daga garin Garam da kuma al’ummar Zhibi da ke karamar hukumar Tafa a jihar Neja.

Garam, inda aka yi garkuwa da mutane 14, yana kan hanyar Sabon-Wuse-Bwari, yayin da Zhib, inda kuma aka yi garkuwa da wasu mutane uku, wani yanki ne na al’umma da ke da iyaka da Dei-Dei, wanda ke karkashin karamar hukumar Bwari ta babban birnin tarayya, FCT.

Wani kwamandan ‘yan banga a Garam, Dantani Daniel, ya ce ‘yan bindigar sun kai hari a unguwar Sabon-Unguwa da ke unguwar da misalin karfe 1 na safe.

Daniel ya kara da cewa “Sun kwashe wadanda abin ya shafa daga gidaje daban-daban suka bar al’ummar cikin kasa da sa’a guda.”

Wani mazaunin garin ya ce maharan sun kai hari gidan wani dan sanda da ke zaune a unguwar inda suka harbe shi.

“An garzaya da shi babban asibitin Kubwa inda yake karbar magani,” in ji shi.