Yan Bindiga Sun Mika Makamai Bayan Tattaunawa – Gwamnatin Plateau

Yan Bindiga Sun Mika Makamai Bayan Tattaunawa – Gwamnatin Plateau

Gwamnatin jihar Filato a ranar Litinin din da ta gabata ta ce wasu ‘yan bindiga da ke addabar al’umomin karamar hukumar Wase da ke jihar sun mika ma gwamnatin jihar dimbin bindigu kirar AK47.

Mai baiwa gwamna shawara na musamman Caleb Mutfwang akan harkokin tsaro kuma kwamandan Operation Rainbow Bridger General Gakji Shippi shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Jos babban birnin jihar.

Shippi ya bayyana cewa mika makaman ya biyo bayan tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnati da ‘yan bindigar.

Ya ce baya ga bindigun AK47, wasu nau’o’in makaman da ‘yan fashin kuma sun mika wuya, wanda hakan ke nuna aniyar samar da zaman lafiya ta hanyar kwance damara.

Ya kara da cewa, ‘yan bindigar ba su mika bindigogin kai tsaye ba saboda fargaba amma sun yi hakan ne ta hanyar shiga tsakani a tattaunawar.

Tare da makaman da suka mika wuya, an kuma kwato wasu makamai da aka mayar da su ba aiki ba,” inji shi.

Shippi ya kara da cewa, ana ci gaba da kokarin karfafa gwiwar ‘yan bindiga da su mika makamansu bisa radin kansu, kuma ana daukar matakan kwato karin bindigogi daga wasu kungiyoyi domin rage kai hare-hare a karamar hukumar Wase.