‘Yan Bindiga Sun Kashe Sarakuna 2 A Jihar Imo

Shaidun gani da ido sun ce bayan harbin kan mai uwa da wabi da ‘yan bindigar suka yi a wajen taron na dan kankanin lokaci da yayi sanadiyyar mutuwar sarakunan, nan take kuma suka bar wajen ba tare wani jinkiri ba. 

Rahotanni daga jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da ba’a tantance ko su waye ba, sun kashe sarakunan gargajiya biyu a wani hari da suka kai a jihar.

‘Yan bindigar sun kai farmakin ne a yayin da ake gudanar da wani taron sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a garin Nnenasa da ke karamar hukumar mulkin Njaba, inda suka bude wuta ba kakkautawa, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar sarakunan biyu.

Wadanda lamarin ya rutsa da su kuwa su ne sarkin al’ummar Okwudor, E. Duruebere, da sarkin al’ummar Ihebinowerre, Sampson Osunwa, dukan su daga karamar hukumar mulkin ta Njaba.

Harbe-harben ‘yan bindigar dai ya sa duk jama’ar wajen tarwatsewa, da kuma arcewa domin tsira da rai, lamarin da kuma ya sa wasu da dama suka sami raunuka.

Shaidun gani da ido sun ce bayan harbin kan mai uwa da wabi da ‘yan bindigar suka yi a wajen taron na dan kankanin lokaci da yayi sanadiyyar mutuwar sarakunan, nan take kuma suka bar wajen ba tare wani jinkiri ba.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Imo ta tabbatar da aukuwar lamarin ta bakin kakakinta Mike Abattam, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN ya ruwaito.

Abattam ya ce yanzu haka ‘yan sanda na gudanar da bincike kan lamarin, domin gano ko su wa ke da hannu a kai harin.

Har kawo yanzu kuma babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan harin.