‘Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun yi garkuwa da mutum 1 a Bauchi
A ranar Juma’a ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a karamar hukumar Toro da ke jihar Bauchi, inda suka kashe wasu matasa biyu tare da yin garkuwa da daya.
Wata majiya daga yankin ta shaida cewa ‘yan bindigar sun far wa garin ne da sanyin safiyar Juma’a, da misalin karfe 1:20 na safe zuwa 2:30 na safe, inda suka yi ta tafiya daga wannan wuri zuwa wancan na tsawon sa’o’i biyu ba tare da wata turjiya ba.
Majiyar ta koka da cewa a duk tsawon wannan samame babu wani jami’in tsaro da ya zo ya kalubalanci su, yayin da ‘yan banga suka rasa yadda za su yi, domin ba za su iya fuskantar babbar wuta ta maharan da ke dauke da muggan makamai ba.
DAILY POSTta wallafa cewa wadanda aka kashe sun hada da Abba da Anas Wanzam yayin da aka yi garkuwa da AdulRahman Abdulrahman Danmalam.
A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yan sandan jihar ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba saboda PPRO, SP Ahmed Wakili bai amsa sakon tes da aka aika masa domin tabbatarwa ba.