‘Yan bindiga sun kashe mutane shida a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutane shida a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kisan mutane shida da wasu ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Faskari da ke jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO), ASP Abubakar Aliyu, ya tabbatar da kisan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Ya ce an kuma jikkata mutane 10 a harin wanda ya faru a kauyen Nasarawa ranar Lahadi.

“A ranar 19 ga watan Fabrairu, da misalin karfe 11:30 na rana, wasu da ake zargin ‘yan bindiga dauke da muggan makamai, dauke da muggan makamai irin su AK-47, sun kai hari kauyen Nasarawa da ke karamar hukumar Faskari.

“Sun harbe mutane shida, suka raunata 10, sannan suka kona gidaje uku da motoci kusan 10,” in ji shi.

Abubakar ya kara da cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Aliyu Musa, ya tura jami’an rundunar da dabarun yaki, aiki da kuma bayanan sirri zuwa wurin.

Ya ce jami’an ‘yan sandan suna ta tseguntawa dazuzzukan dajin domin samun nasarar cafke wadanda suka aikata laifin. (NAN)