Akalla Falasdinawa 165 ne aka kashe tare da jikkata 250 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza.
Aƙalla mutane 14 ne sojojin Isra’ila suka tsare a yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da suka mamaye a cikin wani samame da aka kai cikin dare, in ji ƙungiyar Fursunonin Falasdinu a cikin wata sanarwa.
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce hare-haren da Isra’ila ta kai ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa 21,672, yayin da mutane 56,165 suka jikkata a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba.