Yadda ‘yan sanda ke kama makusantan masu laifi.

Batun kamawa da tsare makusantan wani da ake zargin ya aikata laifi daga jami’an tsaro, abu ne da ya daɗe yana ci wa ‘yan Nijeriya tuwo a ƙwarya.

Masana dai sun ce matakin wanda ya fi yawa a tsakanin ‘yan sandan Nijeriya, ya saɓa wa doka, amma rashin sanin haƙƙi da kuma hanyoyin da mutum zai bi kadin haƙƙinsa ne suka ƙarfafa hakan.

Mutane da dama dai a Najeriya sun sha taka sahun barawo in da jami’an tsaro ke tisa keyar iyaye ko ‘ya’ya ko kuma makusanta wadanda ake zargi da aikata wani laifi a lokacin da wadanda ake zargin suka gudu.

Kamfanin jaridar BBC ta wallaf a Shafinta cewa ta yi hira da Musa Ibrahim, matashi ne wanda ‘yan sanda suka kama kan wani laifin da bai ji bai gani ba irin taskon da ya shiga a lokacin da aka kamashi.

Ya ce “Alaka ta da shi abokina ne sosai, sai jami’an tsaro suka zo nemansa, to da basu same shi sai mu da suka gani a dakinsa, sun tambayemu ina wane yake muka ce bamu san in da ya je ba, to ba tare da sun fada mana dalilin nemansa ba kawai sai suka kama mu suka tafi damu”.

Ya ce sai da suka shafe makonni uku a hannun ‘yan sanda , daga nan sai aka kai su gidan kaso, daga nan ne kuma suka ce sai mu jira a neme mu a kotu domin ayi mana shari’a.

Musa Ibrahim, ya ce,”Haka muka yi ta zama a gidan kaso wanda ya yi laifi bai kawo kansa ba, haka muka yi ta zama har aka yi mana shari’a”.

To ko me dokar ‘yan sanda ta ce a kan irin wannan kame da ‘yan sanda ke yi?

DSP Josephine Ade, ita ce mai magana da yawun ‘yan sandan birnin Abuja, ta ce a sashe na 36 na sabuwar dokar ‘yan sanda ta 2020, ya hana wannan kame da ‘yan sanda ke yi.

Ta ce,” An sanya a allon talla na koanne ofishin ‘yan sanda a kan haramcin irin wannan abu na kama makusancin mai laifi, don kowa ya san hakkinsa”.

DSP Josephine, ta ce, ” Ko shakka ba bu akai masu irin wannan hali, amma a Abuja babban birnin tarayya Najeriya ba a yi idan ma da an yi yanzu an daina”.

Da alama dai kamar yadda jami’an ‘yan sanda ba su san da dokar data hana irin wannan kamen ba koma sun sani suka take, haka suma wadanda ake kamawa ba su san yadda za su bi hakkinsu ba.

Masana shari’a dai sun ce mutum na da damar zuwa kotu don nemawa wani dan uwansa da aka kama ba tare da wani laifi ba hakkinsa.

Yana da kyau mutane su san hakkokinsu don kare kansu daga duk wani abu makamancin hakan da same su.