Yadda masu bin jingin ƙasa suka ji da dakatar da jigilar fasinjoji daga Kaduna zuwa Abuja
Masu bin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja, babban birnin Najeriya sun fara tsokaci kan matakin hukumar sufurin ƙasar na dakatar da jigilar fasinjoji har illa masha Allahu.
Hakan ya biyo bayan wani hari da ake zargin an kai wa wani jirgi da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna, inda fasinjojin da abin ya rutsa da su, suka ce sun ji wata babbar kara ta fashewar wani abu, wadda ta yi sanadin tsayawar jirgin cik.
Jaridar BBC ta wallafa cewa Wani fasinja da ke bin jirgin ƙasan ya shaida mata cewa dakatar da jigilar jiragen kasan a yanzu ta sa dole zai rage yawan tafiye-tafiyen da yake yi zuwa Kaduna daga Abuja, domin kare kansa daga abin da ka je ya zo.
“Dama tsoron yanayin da hanya ke ciki ne ke sa mu ajiye motocinmu mu bi jirgin kasa, amma yanzu ga shi ma bai tsira ba, yanzu haka na so in je Kaduna amma saboda rashin hanya na zauna a gida na haƙura,” in ji shi.
A cewarsa, “Idan ba a samu hanyar jirgin ba nan kusa, dole haka zan kama hanya na bi mota, amma fa za mu hau hanya ne saboda shahada kawai, kuma rashin natsuwa da halin tsaron nan ne yake samu kullum zama cikin taraddadi.
Ya ce tun lokacin da aka samu wannan matsala bai fita daga Abuja ba, yana nan zaune wuri guda domin kare kansa daga fadawa irin wannan matsala.
“Ina cikin Abuja, saboda idan ka fita ba ka san inda za ka fada ba, ni nasan wanda masu garkuwa da mutanen nan suka kama, halin da ya shiga babu daɗin ji ko kadan, dole mutum ya kiyaye kansa,” in ji wannan matafiyi da ya saba bin titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna”.
Shi kuwa wani fasinjan cewa ya yi dama dalili biyu ne ke sa mutane suna bin jirgin ƙasan, na farko sauƙi, na biyu kuma halin da ake ciki na tsaro, mutane na ganin kamar za su fi zama lafiya, amma yanzu dole kowa zai shiga firgici.
A cewarsa “Ya zama wajibi gwamnati ta duba abin da za ta yi kan bangaren tsaro domin su kadai ne dama wadannan hanyoyi guda biyu, kuma ba kowa ne ke da kudin da zai biya ya hau jirgin sama ba.”
Shi ma wannan matafiyin ya ce dole idan ta kama haka zai bi titin mota ya yi tafiya, tun da babu yadda za a yi.
Mutane da dama dai suna bin jirgin ne daga babban birnin Najeriyar saboda yawan hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa kan motoci da ke zirga-zirga kan titi, da kuma sace mutane don neman a biya kudin fansa.